Jirwaye: Yanayin rayuwarmu na bukatar gyara

A wannan makon, filin nan ya amshi bakuncin MALAM IBRAHIM MUSA (+19797394729) E-mail: [email protected] <mailto:[email protected]>; wanda ya yi mana tsokaci game da yanayin rayuwar da muke ciki a halin yau. Ga abin da yake cewa: Jama’a barkanmu da wannan yanayi. Muna addu’a, Allah Ya kawo mana sauki da yalwa a kasarmu baki daya. Yanayin da […]

Jirwaye: Yanayin rayuwarmu na bukatar gyara
Jirwaye: Yanayin rayuwarmu na bukatar gyara

A wannan makon, filin nan ya amshi bakuncin MALAM IBRAHIM MUSA (+19797394729) E-mail: [email protected] <mailto:[email protected]>; wanda ya yi mana tsokaci game da yanayin rayuwar da muke ciki a halin yau. Ga abin da yake cewa:

Jama’a barkanmu da wannan yanayi. Muna addu’a, Allah Ya kawo mana sauki da yalwa a kasarmu baki daya. Yanayin da muke ciki ba sabon abu ba ne kuma ba madauwami ba ne da yardar Allah. Idan mun kara hakuri komai zai zo ya wuce. Hausawa suka ce bayan wuya sai dadi.
Wannan maganar ta yi kama da ayar nan ta cikin ‘Alamnashraha’ da ta yi nuni da yawaitar sauki bayan wahala. Shi ya sa kullum sai ka ji Bahaushe yana cewa Allah Ka yi mana “Alamnashraha.” Wannan tauhidin a dunkule abu ne mai kyau da ya kamata mu lizimci yawaita shi a tsakanin al’umma.
Wani hanzari ba gudu ba, idan an samu tauhidi sai kuma a gyara zamantakewa ko mu’amala. Yau mun samu kanmu a wani irin yanayi da al’umma ta fifita tara gemu a kan taimakon juna. Ba wai ina nufin tara gemu matsala ba ce. Ko kadan ba haka zancen yake ba. Shi gemu abu ne mai kyau kuma cikarsa ya kamata a ganta da yanayin tausayi da jinkan juna. Duk inda gemu da masallatai suka yawaita, ya kamata taimakon juna, aminci da gaskiya su yi tasiri sosai.
Nakan yi mamakin cewa me ya sa a unguwa da take da dubunnan al’umma na rayuwa a ciki, a samu mara lafiya da ciwonsa bai wuce a kashe Naira dubu 60 ba, a yi masa magani, amma sai ya yi tattaki ya je gidan rediyo an yayata shi kafin a samu mai kawo masa tallaf? Ko kuma ka ga magidanci ya rasa abinci, ya fito yana bara a gefen titi domin ya samu masarar da zai kai gida iyali su ci. Yanzu a ce muyi Sallah sau biyar a kullum tare, amma mu zuba ido ciwo ya kashe dan uwanmu a kan abin da idan kowanne masallaci da ke bin jam’i zai ba da Naira 100 zuwa 1000 za a tara kudin da za a ceto shi. Anya wannan zamantakewa ta yi kama da sunnar gemu ta ainihi? To, me muka dauki taruwarmu a masallaci ne?
Kwanan nan na je wani taro a kan yadda za a karbi ’yan gudun hijira daga Syria a garin Tedas. Abin sha’awa, rukuni guda na cocin Katolika su ne suke gaba-gaba wajen karbo bakin da kuma tabbatarwa sun samu rayuwa cikin kwanciyar hankali babu tsangawama. Kada ka ce wai wani kudi ne da su, taimakon juna ba aikin attajirai ba ne har talaka ma ya kamata a gan shi kacokan wajen kyautata yi. Da karo-karo giwa ta fi namun dawa girma. Idan kowa zai ba da daidai gwargwado, za mu iya yi wa kanmu abubuwa da dama, mu magance wa kanmu kangi da fatara. Limaman unguwa ya kamata su koyi darasin hada kan al’umma a kan taimakon kai-da-kai. Mutane su gane cewa yi wa wani yi wa kai ne.
A karshe zan rufe wannan gajeriyar makala da wani labari da na ji Kwamandar Hisbah ta bayar a Rediyon Freedom da aka yi hira da ita, wanda ya faru a kansu. Wata budurwa ce ta fitsare kafarta, babu abin da take sai gantali. Jama’ar unguwa sai abin ya fara damunsu, domin haka sai suka kai kara Hisbah, ta zo ta yi musu maganinta. Kowa dai ya san Hisbah wajen cika aiki. Haka aka hadu runduna guda aka tafi za a kaddamar wa da fitsararriyar unguwa hukunci. Da zuwansu sai yarinya ta ce kada kowa ya shigo mata gida. Idan kuma aka aikata haka za ta kirawo ’yan sanda. Da yake an yi dace akwai dattijai har da mai unguwa a rundunar zartar da hukunci sai aka lallabe ta ta hakura ta bar su suka shiga don yi mata tambayoyi.
Yarinya ta kada baki tana kuka ta fara ba da labarin yadda aka yi ta zama fitsararriya. Wato asali dai mahaifanta sun rasu sun bar ta da kanne maza da mata guda 5. Tun da suka rasu babu daya daga makwabta ko mutanen unguwa da ya taba tuntubra shin ko ya yaran nan suke rayuwa. Da wahala ta ishe su sai ita babbar wadda ake ganin ta fitsare kafa ta shiga neman maza don ta samo wa kannenta abin da za su ci. Ta kudure a zuciyarta cewa su kannenta su zauna gida su yi karatu, ita kuma ta saida kanta ta samo musu abinci su rayu. Da ta gama ba da labari, sai ta kalli mai unguwa ta ce: “Tun da kake ka taba kirana ka tambaye ni yadda muke rayuwa babu uwa babu uba?” Mai unguwa ya sunkuyar da kai. Kwamandar Hisbah ma sai kunya ta kama ta.
Yanzu idan na tambaye ku a nan, shin mun yi wa kanmu adalci da muka bar wannan yarinya ta lalace? Mu fa Musulmai ne, mafi yawanmu masu riko da sunna! Da yawa mata suna shiga yanayin kunci kuma azzaluman mutane daga cikinmu su yi amfani da damar su lalata su, domin sun sani babu yadda za su yi. Maimakon a taimake su tsakani da Allah, sai a mayar da abin ba ni gishiri na ba ka manda. Ita fa yunwa da wahala tana iya sa mutum ya shiga halaka ba don son ransa ba.
Da fatan za mu yi wa kanmu karatun ta-natsu. Sai kuma mako na gaba, inda za mu karkare tambihin nan kashi na biyu.