Jitajita ta sanya mutane daina karbar tsofaffin kudade a Saminaka

A sakamakon yada labarin cewa daga ranar Alhamis 29 ga watan nan, za a daina karbar takardun kudaden da suka tsufa ko suka yage ko aka manna masu gam. Al’ummar da ke zaune a yankin Saminaka da ke Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna, sun dai karbar wadannan kudade. Binciken da wakilinmu ya gudanar dangane da […]

Jitajita ta sanya mutane daina karbar tsofaffin kudade a Saminaka

A sakamakon yada labarin cewa daga ranar Alhamis 29 ga watan nan, za a daina karbar takardun kudaden da suka tsufa ko suka yage ko aka manna masu gam. Al’ummar da ke zaune a yankin Saminaka da ke Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna, sun dai karbar wadannan kudade.

Binciken da wakilinmu ya gudanar dangane da wannan al’amari, ya gano cewa wannan al’amari ya jefa al’ummar yankin cikin mawuyacin hali. Wakilin namu ya gano cewa ‘yan kasuwa da masu gidajen mai da masu tuka motocin haya da yara da suke tallar kayayyakin abinci a yankin duk sun daina karbar wadannan takardun kudade.  Wannan al’amari ya sanya ana samun takaddama tsakanin masu saye da masu sayar da kayayyaki a wannan yanki.

Mutane da dama da wakilin namu ya zanta da su sun yi zargin cewa reshen bankin First Bank da ke garin Saminaka ne ya jawo wannan al’amari, ta hanyar kin karbar tsofaffin kudaden. Mutane da dama sun bayyana cewa sun kai kudaden su zuwa wannan banki, amma sun ki karba.

To amma a lokacin da wakilin namu ya ziyarci bankin ya ganewa idanunsa yadda mutane da dama suka kai tsofaffin kudaden kuma ana karba.

Wani jami’in bankin wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya shedawa wakilinmu cewa ba gaskiya bane cewa an kawo masu tsofaffin kudade sunki karba.

Ya ce, su basu da damar kin karbar tsofaffin kudaden kuma basu san in da mutane suka samo labarin cewa a daina karbar wadannan kudade ba. Ya ce wannan doka tsakanin bankuna ne da babban bankin Najeriya CBN. Kuma abin da dokar ta ce daga ranar 29 ga wannan wata, babban bankin Najeriya zai rika yin cajin kudade ga dukkan bankunan da suka kawo tsofaffin kudade, domin a canza masu a bankin. Sabanin da ake canza masu ba tare da karbar komai ba.

Lokacin da wakilin namu ya tuntubi wani babban jami’i, a babban bakin Najeriya kan wannan al’amari, ya shedawa wakilinmu cewa, wannan doka tsakaninsu ne da bankuna amma bata shafi sauran jama’a ba.

Ya ce, suma bankuna ba a basu umarni su daina karbar tsofaffin kudade ba. Dokar dai ta yi bayanin cewa daga yanzu za a rika yin cajin kudade, ga dukkan bankunan da suka kai wadannan kudade domin a canza masu.