Jiya aka binne George H.W. Bush

Yadda shugabannin Amurka suka ji kan rasuwarsa A jiya Alhamis ce aka binne  gawar tsohon Shugaban Amurka Geroge H.W Bush a kusa da kabarin matarsa Barbara wadda ta rasu a watan Afrilu da ’yarsu Robin a dakin karatunsa da ke Tedas. George Bush ya rasu ne a ranar Juma’ar makon jiya a Jihar Tedas, yana da […]

Jiya aka binne George H.W. Bush
  • Yadda shugabannin Amurka suka ji kan rasuwarsa

A jiya Alhamis ce aka binne  gawar tsohon Shugaban Amurka Geroge H.W Bush a kusa da kabarin matarsa Barbara wadda ta rasu a watan Afrilu da ’yarsu Robin a dakin karatunsa da ke Tedas.

George Bush ya rasu ne a ranar Juma’ar makon jiya a Jihar Tedas, yana da shekara 94, shi ne Shugaban Amurka na 41.

Shugaba Bush babba, kamar yadda ake yi masa lakabi, shi ne ya jagoranci kawo karshen yakin cacar baki, ya kuma jagoranci yakin da ya tilasta wa Sadam Hussein ficewa daga Kuwait a 1991.

Bush, ya yi wa’adi daya ne kacal a kan mulki daga 1989 zuwa1993.

Daga cikin wadanda suka yi aiki da gwamnatinsa, akwai tsohon Sakataren Harkokin Wajen Amurka James Baker da tsohon Sakataren Tsaron Amurka kuma Mataimakin Shugaban Kasa Dick Cheney, sun bayyana a gidan talabijin na Fod News ranar Lahadi, inda Baker ya bayyana Mista Bush a matsayin daya daga cikin shugabannin kasar masu nagarta.

Tsohon babban hafsoshin soja kuma mai bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Colin Powell, ya ce Shugaban Kasa na 41, kuma matukin jirgin sama lokacin Yakin Duniya na Biyu, ya san illar yaki don haka ne ya yi kokarin ganin bai yi amfani da sojoji ba a Yakin Tekun Fasha na farko kamar yadda Muryar Amurka ta ruwaito.

A ranar Litinin ce aka ajiye gawar Bush a Majalisar Dokokin Amurka, ta kasance a wurin har zuwa  shekaranjiya Laraba, inda aka gudanar da babbar karramawa ta kasa a Majami’ar National Cathedral, kafin a mayar da gawar zuwa Jihar Tedas inda aka binne shi a ginin dakin na karatunsa.

Mun yi babban rashi – Trump

Shugaban Amurka, wanda ya sanar da shekaranjiya Laraba a matsayin ranar makokin tsohon shugaban, ya bayyana rasuwar Bush babba a matsayin wani babban rashi  ga kasar, “Da ni da uwargidata Melania mun shiga cikin sahun masu makokin rasuwar tsohon Shugaban Kasa George H.W. Bush. Ta hanyar amfani da kokarinsa da nuna tabbaci da imani da kasar Amurka, Shugaba Bush ya taimaka wajen nusar da dimbin mutanen Amurka wajen yin aiki tukuru domin ciyar da kasar nan gaba. Sannan ya taimaka wajen nuna girma da iko da damarmakin Amurka a idon duniya,” inji shi.

Amurka ta rasa dan kasa nagari – Barrack Obama

A nasa jawabin, tsohon Shugaban Amurka, Barrack Obama ya bayyana Bush babba a matsayin dan kasa nagari, wanda kasar Amurka da mutanenta suka rasa, “Lallai Amurka ta rasa dan kasa nagari, wanda ya yi aiki ba dare ba rana cikin natsuwa. A daidai lokacin da muke makokin rasuwarsa, muna yin godiya kuma a gare shi. Muna taya iyalan Bush jimamin rashinsa, da kuma duk wadanda Bush da Barbara suka taimaka a rayuwa,” inji shi

Mun yi rashin mahaifi – Bush karami

Tsohon Shugaban Amurka Bush karami a nasa ta’aziyar, ya bayyana cewa shi da iyalansa sun yi rashin babban mahaifi, “George H.W. Bush mutum ne mai kima da sanin ya kamata, kuma cikakken uba ne da duk wani da ko ’ya za ta su so su samu. A madadin iyalan Bush, muna matukar godiya ga dukan wadanda suka nuna damuwarsu kuma suka yi addu’a ga mahaifinmu da kuma ta’aziyar da suka aiko mana da sauran ’yan kasa baki daya,” inji shi.

Muna godiya ga ayyukan da Bush ya mana – Bill Clinton

A nasa jawabin, Bill Clinton godiya ya yi ga Bush babba bisa abubuwan alheri da ya bari, “Da ni da matata Hillary muna jimanin rasuwar Shugaba George W. H. Bush, kuma muna godiya gare shi bisa ayyukan alheri da ya dade yana yi, da kauna da abota da ya nuna mana. Ina godiya gare shi na lokacin da muka yi tare, sannan zan ci gaba da rike abotarmu a matsayin babbar kyauta a rayuwata,” inji shi.