John Mike Obi yana shirin barin Chelsea

dan kwallon tsakiya a kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles da yanzu haka yake buga wa kulob din Chelsea na Ingila kwallo John Mikel Obi yana shirin barin kulob din don komawa na Al Ain FC da ke Hadaddiyar Daular Larabawa. Rahotannin da ke fitowa daga Ingila sun nuna kulob din Al Ain yana […]

John Mike Obi yana shirin barin Chelsea
John Mike Obi yana shirin barin Chelsea

dan kwallon tsakiya a kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles da yanzu haka yake buga wa kulob din Chelsea na Ingila kwallo John Mikel Obi yana shirin barin kulob din don komawa na Al Ain FC da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.

Rahotannin da ke fitowa daga Ingila sun nuna kulob din Al Ain yana shirin saye Obi ne a kan zunzurutun Dala miliyan 12 kwatankwacin Naira biliyan 2 da miliyan 628. dan kwallon ne da kansa ya sanar da haka, amma kawo yanzu babu wani bayani da aka samu daga kulob din Chelsea ko na Al Ain a kan wannan batu.
Sai dai dillalin Mike Obi Babawo Mohammed ya tabbatarwa manema labarai cewa John Mikel Obi ya amince ya koma kulob din na Al Ain abin da suke jira kawai shi ne amincewar kulob din Chelsea.
“Mikel Obi ya amince da yarjejeniyar da suka kulla a tsakaninsa da kulob din, abin da ya rage kawai shi ne amincewar kulob din Chelsea da na Al-Ain a kan kudin da za su sayar da shi”, inji Babawo Mohammed.
Mikel Obi dai ya yi wa Chelsea wasanni har sau 224 inda ya samu nasarar lashe kofin zakarun kulob-kulob na Turai watau (Champions League) sau daya da kofin Europa sau daya da gasar firimiya sau biyu da kofin Carling sau biyu da kofin Community sau daya da kuma kofin kalubale (FA) sau daya.
Tuni kyaftin din Ghana Asamaoh Gyang da yanzu haka yake buga wa kulob din Al Ain kwallo ya yi maraba da zuwan Mikel Obi a wata hira da aka yi da shi.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram