John Terry ya zama Mataimakin Kocin Aston Billa

Kulob din Aston Billa da ke Ingila ya bayar da sanarwar nada sababbin manajoji. Sanarwar ta nuna an zabi Dean Smith a matsayin sabon koci yayin da aka zabi tsohon dan kwallon Chelsea John Terry a matsayin mataaimakinsa.  Sannan kulob din ya zabi Jesus Garcia Piterach a matsayin Daraktan kula da harkokin wasanni. John Terry […]

John Terry ya zama Mataimakin Kocin Aston Billa

Kulob din Aston Billa da ke Ingila ya bayar da sanarwar nada sababbin manajoji.

Sanarwar ta nuna an zabi Dean Smith a matsayin sabon koci yayin da aka zabi tsohon dan kwallon Chelsea John Terry a matsayin mataaimakinsa.  Sannan kulob din ya zabi Jesus Garcia Piterach a matsayin Daraktan kula da harkokin wasanni.

John Terry ya taba buga wa kulob din Aston Billa kwallo kafin ya canza sheka zuwa kulob din Chelsea.  A kwanakin baya ne ya bayyana sanarwar daina yin kwallo da hakan ya ba kulob din Billa damar daukarsa a matsayin mataimakin koci.

Ana sa ran John Terry zai yi amfani da kwarewa wajen farfado da martabar kulob din Aston Billa da ke buga gasar rukunin ’yan dagaji a Ingila da aka fi sani da (Championship).