Jonathan a Jam’iyyar APC?
Tambaya ce wani ya aiko min da ita, yana cewa wai shin muna kuwa da jam’iyyun siyasa a Najeriya a halin yanzu? Ya yi tambayar ce ganin yadda aka dama, aka kuma sha a zaben da aka yi kwanan nan na Gwamnan Jihar Bayelsa, wato jihar tsohon Shugaban Kasa Goodlukc Jonathan, inda aka yi kiri-da-muzu […]
Tambaya ce wani ya aiko min da ita, yana cewa wai shin muna kuwa da jam’iyyun siyasa a Najeriya a halin yanzu? Ya yi tambayar ce ganin yadda aka dama, aka kuma sha a zaben da aka yi kwanan nan na Gwamnan Jihar Bayelsa, wato jihar tsohon Shugaban Kasa Goodlukc Jonathan, inda aka yi kiri-da-muzu aka zabi dan takarar Jam’iyyar APC maimakon dan takarar Jam’iyyar PDP, jam’iyyar da ke mulkin jihar tun daga 1999 da aka soma wannan zangon tsarin dimokuradiyya da muke ciki.
Duk da cewa wadansunmu sun fahimci yadda aka gudanar da wancan zabe da kuma dalilan da suka sanya aka samu wannan ‘canjin’ a jihar ta Bayelsa, bisa ga dukkan alamu, wadansu na cikin kuncin rashin sani dangane da yadda tsohon Shugaba Jonathan zai bari a yi masa wannan yankan kauna a jiharsa, a kuma lokacin da ake jin cewa ya dace ya yi hobbasa ya kame jiharsa, domin ya zama ana damawa da shi a jihar da kuma kasa baki daya dangane da ‘sana’arsu ta siyasa.’ Ga masu irin wannan tunani, abin da ba za su gane ba shi ne da sanin tsohon Shugaba Jonathan aka yi wannnan kida da rawar a Jihar Bayelsa, ba Jam’iyyar APC ce aka zaba ba, ba kuma Jam’iyyar PDP ce aka kada ba, haka kuma ga Shugaba Jonathan, duk inda ta fadi sha a wancan zabe, abin da kurum zai yarda da shi, shi ne, dan takarar PDP ya ci zabe, tunda nasa dan takarar bai samu wannan dama ba, musamma in dan takarar APC din ya amince cewa Shugaba Jonathan shi ne ‘Ubangidansa,’ ko da kuwa ba jam’iyyarsu guda ba!
Ga wanda bai gane haka ba, to kuwa bai gano lagon tsarin gudanar da siyasar kasar nan ba, bai kuma gano lamon da ’yan siyasa ke yi ba ko kuma ‘hawainiyar’ da suke komawa domin su samu ganima da garabasar siyasa da mukamai.
Duk wannan ba shi ne matsalar ba, matsalar ita ce me ya sa ’yan siyasar Najeriya ke yin yadda suke yi a cikin irin wannan lamari, me kuma yake kara wa darajarsu ko kuma ta yaya yin hakan ke taimakon kasa da ci gabanta? Kamar yadda na sha fada a baya ne ai, yanzu in mutum ya natsu zai ga cewa ba wata jam’iyya wai ita APC ko kuma PDP, ko wasu jam’iyyu can daban. Duk abin daya ne. Yau dan siyasa in yana wannan jam’iyya, gobe za a ga yana waccan, abin da ke da muhimminci dai a wurin ’yan siyasa bai wuce, ana yi da ni ba.
Na san wadansu za su ce, ai ita da ma siyasa haka ta gada, kwamacala, rashin kan gado, barna da lalaci da lalatawa. Wadansu na iya cewa ai rashin madafa shi ne siyasa ko kuma munafunci da almundahana da rashin sanin makoma. Amma a duk lokacin da mutum ya natsu, ya yi nazari, ya kuma fuskanci yadda wadansu al’ummomi a wasu kasashe ke gudanar da siyasar da yadda can kwamacalar da kwadon siyasa mai ciwuwa ne, ba na yardawa ba, sai ya kara natsuwa cikin aminci da cewa, kila dai siyasar Najeriya ba ta da kan gado ne. Kila ’yan siyasar Najeriya ne ba su san yadda ake zuba tuwon siyasa, kabaki-kabaki a cikin kwarya ba. Kila kasar Najeriya ce ba ta iya shuka iri a tata gonar siyasar ba ko kuma ba ta da irin na kwarai, kamar yadda ake shuka shi a wasu kasashe, ba tare da an sa masa takin zamani ba!
Me ya sa na ce haka? Ba komai ya jawo hankalina ga haka ba face irin yadda na ga siyasar Najeriya a cikin ’yan kwanakin nan ta dauki sabon salo, an shiga hayagaga, musammin ganin yadda jam’iyyar nan mai lema ta shiga cikin rudu saboda yadda tsohon Shugaba Jonathan ya yi mata-sakiyar-da-ba-ruwa a Jihar Bayelsa, sa’annan kuma wadansu na ta murna cewa ai gara Shegiyar Uwa ta mutu, a share ta da Tsintsiya, saboda ingancin mulki irin na Shugaba Buhari.
Abin tambaya shi ne, wane irin tunani ne wannan? Alhali kuma a duk lokacin da ake sharewa da kwashewa sai na ga ana sake zuba dattin a cikin dakuna ko falon jam’iyyar tsintsiya. Ni kuwa a nawa tunanin, kai ko yaro dan shekara takwas ka tambaya zai bayyana maka cewa, duk inda aka yi amfani da tsintsiya aka yi shara, dattin nan, kwandon shara ko bola ake zuba shi, ba wai a kai shi cikin uwar daki ba, ana yi masa goma sha tara ta arziki, kamar yadda muke gani a halin yanzu!
To wai mene ne asasi? Me ya jawo wannan tabargaza a siyasarmu? Me ya sa mu kullum muke shiga cikin daki ido rufe? Me ya sa za a sharo dattin lalatattar Lema da Tsintsiya, amma a sake zuba dattin a dakin mai shara?