Jonathan bai kyauta ba – APC da Jama’atu

Sai dai kuma babbar jam’iyyar adawa, wato APC ta ce Shugaba Jonathan bai kyauta ba da ya kaddamar da takararsa kwana daya da kashe dalibai 48 a Potiskum ta Jihar Yobe, inda ta zargi Shugaban da tikar rawa a daidai lokacin da ake alhinin daliban da sauran wadanda mayakan Boko Haram suka kashe. Kakakin Jam’iyyar […]

Jonathan bai kyauta ba – APC da Jama’atu

Sai dai kuma babbar jam’iyyar adawa, wato APC ta ce Shugaba Jonathan bai kyauta ba da ya kaddamar da takararsa kwana daya da kashe dalibai 48 a Potiskum ta Jihar Yobe, inda ta zargi Shugaban da tikar rawa a daidai lokacin da ake alhinin daliban da sauran wadanda mayakan Boko Haram suka kashe.

Kakakin Jam’iyyar Alhaji Lai Mohammed ya fadi a wata sanarwa cewa, “Tun da Shugaban kasar ya zabi ya yi shagali a lokacin da ake juyayi a kasa, to ya wajaba ’yan Najeriya su shirya wa bikin faduwarsa a zaben badi,” inji Lai.
Ya ce, “Yau jihohi uku na Arewa maso Gabas suna cikin hadarin komawa karkashin Boko Haram, an tilasta sama da mutum dubu 650 gudun hijira a wadannan jihohi. Amma duk da haka Shugaba Jonathan yana cewa Najeriya ya sanya a gaba fiye da komai, karya fure take yi ba ta ’ya’ya. A gaskiya Jonathan kansa kawai ya sani a kowane lokaci.”
Jam’iyyar APC ta ce lokacin da aka kashe dalibai 60 a Kwalejin Tarayya ta Buni Yadi a Fabrairun bana, Shugaba Jonathan bai ziyarci wurin don ta’aziyya da jajanta wa iyalan yaran ba. Haka lokacin da bam ya tashi a Nyanya da ya halaka mutum 80 a Afrilun bana, Shugaba Jonathan kasa da awa 48 ya tafi Kano ne ya rika tikar rawa, kuma a ranar ce aka sace ’yan matan makaranta a Chibok, lamarin da jami’an gwamnatinsa suka rika karyatawa sai bayan kwana 19 suka yarda an sace su din. “Wannan ya nuna Shugaban kasa ya ginu wajen fifita bukatun siyasarsa a kan bukatun ’yan Najeriya,” inji APC.
Ita ma kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta soki Shugaba Jonathan da nuna rashin damuwa da halin da talakawan Najeriya suke ciki, wadanda ake ta kashe su a kasar nan ba tare da an dauki matakan kirki don kare rayukansu ba.
Babban Sakataren Jama’atu Dokta Khalid Aliyu Abubakar ya shaida wa gidan rediyon BBC haka bayan da Shugaba Jonathan ya kaddamar da takararsa a daidai lokacin da ’yan Boko Haram ke ci gaga da kai hare-hare a sassan kasar nan.
Ya ce, “Babu wani mutum mai tunani da zai kaddamar da takararsa a daidai lokacin da ake ta kashe mutane. Ba mu ji dadi ba kuma ba mu goyon bayan haka.
Wadansu kungiyoyin kare hakkin dan Adam da dama sun soki bikin bayyana aniyar takarar na Shugaba Jonathan bayan awanni da kisan dalibai a Yobe.
kungiyoyin na ganin bai kamata Shugaban ya kaddamar da aniyarsa kwana daya da kashe dalibai 48 a wani harin kunar bakin wake da aka kai a makarantarsu da ke Potiskum ba. Kuma sun nuna rashin dacewar bikin ganin yadda kungiyar Boko Haram ke ci gaba da kwace garuruwa a Arewa- maso Gabas.