Jonathan da Biya sun gana kan Boko Haram a Faransa
Shugaban Goodluck Jonathan na Najeriya ya gana da takwaransa na Kamaru Paul Biya, a kasar Faransa a wani yunkuri na lalubo hanyoyin da za su inganta tsaron iyakokin kasashensu.Taron, wanda Shugaban Faransa Francois Hollande ya kira a birnin Paris, ya kuma tattauna batun yadda zai shawa kan matsalar ’yan kungiyar Boko Haram. A baya dai […]
Shugaban Goodluck Jonathan na Najeriya ya gana da takwaransa na Kamaru Paul Biya, a kasar Faransa a wani yunkuri na lalubo hanyoyin da za su inganta tsaron iyakokin kasashensu.
Taron, wanda Shugaban Faransa Francois Hollande ya kira a birnin Paris, ya kuma tattauna batun yadda zai shawa kan matsalar ’yan kungiyar Boko Haram.
A baya dai an shirya shugabannin biyu za su gana a kasar Kamaru, amma hakan bai yuhu ba. Wasu dai na ganin dalilin da ya sa hakan bai faru ba, bai rasa nasaba da kin amincewar da gwamnatin Kamaru tayi, a baya, na ba dakarun Najeriya damar shigowa cikin kasarta domin bin sahun ’yan kungiyar Boko Haram da suke ketarawa iyakokin kasar. Hakan ya sa wasu suka fara yi wa kasar kallon mai ba ’yan ta’adda mafaka. A baya-bayannan ma wasu sun yi zargin ’yan matan makarantar sakandaren garin Chibok da ’yan Boko Haram suka sace, an ketara da su cikin kasar wanda ke iyaka da Jihar Barno ta Najeriya.
Wannan ya sa Ministan Sadarwar kasar Issa Tchiroma Bakary kiran wani taron manema labarai, inda ya musanta cewa ’yan matan na Kamaru. Ya ba da tabbacin cewa kasar ba mafaka ce ta kungiyoyin ’yan ta’adda ba. Ya ce dalili da haka ne kasar take duk wani kokari don hada gwiwa da kasashen da ke makwabtaka da ita domin su murkushe ayyukan ’yan ta’adda.