…Jonathan da Buhari sun kulla yarjejeniya
Shugaba Goodluck Jonathan na Jam’iyyar PDP da Janar Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC da sauran ’yan takarar Shugaban kasa 12 sun kulla yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya. Yarjejeniyar mai taken: “Yarjejeniyar Abuja,” an sanya mata hannu ne a shekaranjiya Laraba a wajen wani taron fadakarwa kan zabe ba tare da tashin hankali ba da ofishin […]
Shugaba Goodluck Jonathan na Jam’iyyar PDP da Janar Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC da sauran ’yan takarar Shugaban kasa 12 sun kulla yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya.
Yarjejeniyar mai taken: “Yarjejeniyar Abuja,” an sanya mata hannu ne a shekaranjiya Laraba a wajen wani taron fadakarwa kan zabe ba tare da tashin hankali ba da ofishin Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro da na Mashawarcin Shugaban kasa kan Hulda Tsakanin Jam’iyyun Siyasa suka shirya.
Dukkan ’yan takarar Shugaban kasar sun amince da yarjejeniyar kuma suka sanya mata hannu.
Shugaban Taron Cif Emeka Anyaoku wanda ya karanta yarjejeniyar zaman lafiyar, ya nanata cewa Yarjejeniyar Abuja tana magana ne a kan zaben bana.
Cif Anyaoku ya karanta yarjejeniyar kamar haka: “Yarjejeniya tana cewa: “Mu jam’iyyun siyasa da aka ambata da ke takarar babban zaben 2015; muna shirye mu dauki matakan rigakafi domin hana tarzomar a gabani ko lokaci ko bayan zabe.”
“Sannan a shirye muke mu samar da yanayi na lumana da zaman lafiya ga zaben na 2015;
tare da kara jaddada kudirinmu na bin tsarin mulki Najeriya cikin shaukin tabbatar da hadin kai da kasancewar Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa.”
Yarjejeniyar ta kara da cewa: “A shirye muke mu kauce wa duk wata dabi’a ko hali da zai sanya harkokin siyasa da tsaron kasa a cikin hadari; kuma mun shirya domin fifita bukatun kasa a kan bukatunmu ko na jam’iyyunmu.”
Yarjejeniya ta ci gaba da cewa: “Muna sake jaddada kudirinmu na cikakkiyar biyayya ga ka’idoji da dokokin da suke kunshe cikin dokokin zabe a Najeriya. Don haka mun dauki alkawura masu zuwa ga kanmu da jam’iyyunmu cewa:
“1. Za mu rika gudanar da kamfe ne kan batutuwa a matakin kasa da jiha da kananan hukumomi. A kan haka mun yi alkawarin daina kamfe da zai shafi tunzurawa a fagen addini ko kabilanci ko yare mu da kanmu ko wakilan da ke aiki a madadinmu.
2. Za mu kauce daga yin furuci ko bayani ko jawabai ko duk wani kalami da sunanmu ko na jam’iyyunmu da zai iya tunzurawa a yi tashin hankali kafin ko lokaci ko bayan zaben.
“3. Tilasta mu fito fili mu la’anci duk wata magana ta tunzurawa tare da adawa da duk wani tashin hankali da ya shafi zabe koda magoya bayanmu ne suka yi ko abokan adawa.
4. Za mu sadaukar da kanmu da jam’iyyunmu su rika sanya ido tare da tabbatar ana aiki da wannan yarjejeniya, idan zai yiwu a karkashin kular wani kwamitin zaman lafiya na kasa da zai kunshi dattawan da ake girmamawa maza da mata da sarakuna da shugabannin addini.
5. Dukkan hukumomin gwamnati ciki har da INEC da hukumomin tsaro su yi aiki ba tare da nuna goyon baya ga kowane bangare ba.”
Tun farko a jawabin Shugaba Jonathan ya ce rikicin bayan zabe ba lallai ne ya zamo magudin zabe ne ya jawo shi ba.
Ya ce, rikicin zabe kodai yana faruwa ne sakamakon kalaman tunzurawa na ’yan siyasa ko wa’azin kiyayya na shugabannin addini da kalaman shugabannin kabilu da na yaruka.
Ya kawo misali da rikicin bayan zabe da ya faru a jihohin Bauchi da Kano inda ya ce, ya samu kashi 16 da 15 ne kawai a zaben 2011, inda ya ce ba a yi tashin hankali ba a inda ya samu kashi 50 cikin 100 ba.
Tsohon Babban Sakataren Majalisar dinkin Duniya Mista Kofi Annan ya bukaci Najeriya ta tabbatar ta gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali, inda ya yi gargadin cewa tashin hankali na iya kawo koma baya ga daukacin Afirka.
“Duk abin da ya shafi Najeriya ya shafe mu gaba daya, ba ma Afirka ta Yamma kadai ba daukacin Afirka,” Kofi ya shaida wa mahalarta taron.
Ya ce “Duniya ta zuba wa Najeriya ta zuba ido. Nasarar Najeriya a zabe mai zuwa zai kasance nasarar Afirka ne. Najeriya c eke rike da makomar Afirka.”
Shi ma Janar Muhammadu Buhari ya nuna illar da tashin hankali lokacin zaben zai iya jawo wa Najeriya.