Jonathan da Buhari sun sake yarjejeniyar zaman lafiya
Manyan ’yan takarar Shugaban kasa a zaben gobe sun sake sanya hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja. Kwamitin Zaman Lafiya na kasa ne ya tsara Yarjejeniya wadda Shugaba Jonathan, dan takarar Jam’iyyar PDP da babban mai kalubalantarsa Janar Muhammadu Buhari dan takarar Jam’iyyar APC suka sanya mata hannu a jiya Alhamis. Yarjejeniyar kamar […]
Manyan ’yan takarar Shugaban kasa a zaben gobe sun sake sanya hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja.
Kwamitin Zaman Lafiya na kasa ne ya tsara Yarjejeniya wadda Shugaba Jonathan, dan takarar Jam’iyyar PDP da babban mai kalubalantarsa Janar Muhammadu Buhari dan takarar Jam’iyyar APC suka sanya mata hannu a jiya Alhamis.
Yarjejeniyar kamar wadda suka sanya mata hannu a ranar 14 ga Janairun bana, ta kunshi daukar alkawari daga bangarorin biyu cewa za su kauce wa yin duk wani abu da zai jawo tashin hankali a lokacin zaben da bayansa.
Kwamitin Zaman Lafiya na kasa yana karkashin jagorancin tsohon Shugaban Gwamnatin Soja Janar Abdulsalami Abubakar ne, kuma an sanya hannu kan yarjejeniyar ce a gaban idonsa.
An sanya hannu kan yarjejeniyar ce a otel din Transcorp Hilton Hotel, kuma ’yan takarar shugabancin kasar biyu sun samu rakiyar shugabannin jam’iyyunsu wato Ahmadu Mu’azu na PDP da John Oyegun na APC.
Manyan ’yan takarar biyu a wani taro da ya gudana karkashin tsohon Babban Sakataren kasashe Rainon Ingila, Emeka Anyaoku a ranar 14 ga Janairu sun fito sun yi jawabin sukar tashin hankali tare da bayyana sadaukarwarsu wajen gudanar da zabe cikin lumana.
Sauran jam’iyyun da suka sanya hannu a yarjejeniyar ta baya sun hada da AA da AD da UDP da UPP da ADC da kuma HDP.
Taron ya zamo sila na hada ’yan takarar biyu, Jonathan da Buhari bayan fara kamfe a zaben mai muhimmanci da aka rika sukar juna.
Shugabannin biyu sun rungume juna bayan gabatar da jawabansu na suka tashin hankali. Sai dai daga baya APC da PDP sun rika zargin juna da keta yarjejeniyar.