Jonathan da Wike sun kaurace wa kaddamar da yakin neman zaben Atiku
An kaddamar da takarar ne ranar Laraba a Abuja
Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan da Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike tare da ’yan bangarensa sun kaurace wa bikin kaddamar da yakin neman zaben dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.
An kaddamar da takarar ce a Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa da ke Abuja ranar Laraba, kuma ba a ga Jonathan ba, duk da cewa akwai sunansa a kwamitin.
- Za mu tabbatar an yi zaben 2023 cikin lumana – Shugaban ‘Yan Sanda
- Yau ce ranar fara yakin neman zaben 2023 a Najeriya
An dai fara gagarumin bikin ne da kaddamar da wasu littattafai guda uku a kan dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar.
Litattafan sun hada da; “Tarihin Atiku Abubakar” da kuma “Shari’un Kundin Tsarin Mulki a Najeriya (2004 zuwa 2007): Shari’o’in Atiku Abubakar” sai kuma “Sauya fasali a matsayin hanyar kawo hadin kai da ci gaban kasa”.
Sai dai daga cikin wadanda suka halarci bikin akwai Gwamnonin jihohin Bauchi (Bala Mohammed) da na Sakkwato (Aminu Waziri Tambuwal) da na Taraba (Darius Ishaku) da na Delta kuma Mataimakin dan takarar (Ifeayni Okowa) da na Akwa Ibom (Udom Emmanuel) da na Bayelsa (Douye Diri) da na Edo (Godwin Obaseki) da kuma na Adamawa (Ahmadu Fintri).
Sauran sun hada da tsohon Shugabanin Majalisar Dattijai, Abubakar Bukola Saraki da Anyim Pius Anyim da David Mark da kuma tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na’aba.
Kazalika, tsohon Shugaban jam’iyyar na kasa, Uche Secondus, da mai rikon mukamin shugabancinta a yanzu, Ambasada Damagun, sun halarci taron.