Jonathan ga Buhari: Ka fara bincike tun daga 1960

Shugaba mai barin gado Dokta Goodluck Jonathan ya ce bai kamata gwamnatin Buhari mai kama aiki a yau ta takaita bincikenta a kan gwamnatinsa (Jonathan) ba, kamata ya yi ta faro binciken tun daga lokacin da muka samu ’yanci wato daga 1960. Dokta Jonathan ya fadi haka ne a jawabinsa wajen zaman karshe na Majalisar […]

Jonathan ga Buhari: Ka fara bincike tun daga 1960
Jonathan ga Buhari: Ka fara bincike tun daga 1960

Shugaba mai barin gado Dokta Goodluck Jonathan ya ce bai kamata gwamnatin Buhari mai kama aiki a yau ta takaita bincikenta a kan gwamnatinsa (Jonathan) ba, kamata ya yi ta faro binciken tun daga lokacin da muka samu ’yanci wato daga 1960.

Dokta Jonathan ya fadi haka ne a jawabinsa wajen zaman karshe na Majalisar Zartarwarsa a shekaranjiya Laraba a Abuja, inda ya ce yana sane da kiraye-kirayen da wasu ’yan Najeriya ke yi kan a gudanar da bincike. Ya ce idan gwamnati mai kama aiki a yau za ta yi gaskiya, to kada ta binciki gwamnatinsa ita kadai.
Ya nanata cewa zai zamo huce-haushi a binciki gwamnatinsa ita kadai. Ya ce akwai abubuwa da dama da za a bincika tun daga basussukan da ake bin jihohi da kuma bashin da ake bin kasar nan tun daga 1960 zuwa yanzu.
“Wasu mutane ma suna kiran a binciki gwamnatina, amma ina jin a Najeriya akwai abubuwa da dama da za a bincika, abubuwa da dama, hatta bashin da ake bin jihohi da bashin da ake bin kasar nan tun daga 1960 zuwa yanzu. Sun ce gwamnatin Jonathan ne ta ciyo wadannan basussuka,” inji shi.
Ya kara da cewa: “Na yi imani duk wanda zai zo ya yi bincike ya tabbatar ya fara wannan bincike ya hada da gwamnatocin da suka gabaci na Jonathan. Idan ba haka ba, a wurina ya zama huce-haushi da cin dunduniya ke nan. Idan muna da gaskiya ba gwamnatin Jonathan kadai za a bincika ba.”
Wani abin sha’awa da ya faru kafin taron shi ne yadda Minista Sufurin Jiragen Sama Osita Chidoka ya je wurin taron Majalisar Zartarwar a kan keke.
Chidoka ya shaida wa manema labarai na fadar Shugaban kasa cewa ya hau keke zuwa taron na karshe domin ya karfafa dabi’ar cewa yin amfani da dukkan abubuwan sufuri na da muhimmanci.
Ya ce yana jin dadi da ya yi aiki a karkashin gwamnatin Jonathan “Mafi muhimmanci dai shi ne mun yi namu kokarin za mu gusa. Shugaban kasa ya bayar da damar karfafa dimokuradiyya,” inji shi.
A yau ne Jonathan yake mika wa Shugaba Muhammadu Buhari ragamar mulki bayan ya fadi a zaben ranar 28 ga Maris da ya gabata.