Jonathan ga ’yan siyasa: Kada mu rika fada kamar ’yan tasha
Ganin yadda zaben shekarar 2015 ke kara gabatowa ne Shugaba Goodluck Jonathan ya bukaci ’yan siyasa su sanya Najeriya a zuciyarsu, sannan su guji fada kamar yadda ’yan tasha suke yi.Jonathan ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da Cibiyar ‘Kukah Centre’ a Abuja a ranar Talata.Makasudin kafa wannan cibiyar shi ne don […]
Ganin yadda zaben shekarar 2015 ke kara gabatowa ne Shugaba Goodluck Jonathan ya bukaci ’yan siyasa su sanya Najeriya a zuciyarsu, sannan su guji fada kamar yadda ’yan tasha suke yi.
Jonathan ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da Cibiyar ‘Kukah Centre’ a Abuja a ranar Talata.
Makasudin kafa wannan cibiyar shi ne don inganta imani da yadda za a samar da shugabanci nagari da kuma gyaran zuciya.
Shugaban kasar ya ce siyasa ba kawai ’yan siyasa su rika zagin junansu ba ne, ta shafi yadda za a samar da ci gaba da kuma tattauna batutuwa masu ma’ana da za su dora kasar nan a kan turba mai kyau mai dorewa.
“Abin da muke dauka dimokuradiyya ba shi ne dimokuradiyya ba, domin mun dauka takaddama ko asakala ko fada kamar yadda ’yan tasha suke yi su ne dimokuradiyya.” Inji shugaba n kasa.
Jonathan ya bukaci ’yan siyasa su rika ganin 2015 a matsayin shekarar da za su mayar da hankali don karfafa dimokuradiyya da kuma samar da hadin kai.
Ya ce ya kamata a karfafa dimokuradiyya ta hanyar muhawara mai tsabta da samar da sabbin hanyoyi kawo ci gaba da kishin kasa da kuma zaman lafiya.