Jonathan na amfani da addini wajen raba kan ’yan Najeriya – Yaro Makama
Shugaban Jam’iyyar PDP na farko a Jihar Kaduna kuma jigo a Jam’iyyar APC a yanzu Alhaji Audi Yaro Makama ya zargi Shugaba Goodluck Jonathan da amfani da bambancin addini da kabilanci wajen raba kan ’yan Najeriya. Alhaji Yaro Makama ya ce akwai bukatar ’yan Najeriya su tashi tsaye su kawar da gwamnatinsa da jam’iyyarsa ta […]
Shugaban Jam’iyyar PDP na farko a Jihar Kaduna kuma jigo a Jam’iyyar APC a yanzu Alhaji Audi Yaro Makama ya zargi Shugaba Goodluck Jonathan da amfani da bambancin addini da kabilanci wajen raba kan ’yan Najeriya.
Alhaji Yaro Makama ya ce akwai bukatar ’yan Najeriya su tashi tsaye su kawar da gwamnatinsa da jam’iyyarsa ta PDP daga mulki a zaben 2015.
Alhaji Yaro ya bayyana haka ne a karamar Hukumar Kagarko lokacin da yake jawabi ga magoya bayan Jam’iyyar APC a lokacin da mai neman tsayawa takarar Gwamnan jihar Alhaji Isah Mohammad Ashiru ya ziyarci yankin.
Ya ce, ’yan siyasa musamman Shugaban kasa Jonathan na daga cikin masu amfani da addini da kabilanci wajen raba kan jama’a. “Muna fata guguwar canji za ta yi gaba da Shugaban kasa da sauran gwamnatocin PDP har da na Jihar Kaduna a zaben 2015. Akwai bukatar ’yan Najeriya su gane cewa babu wanda zai iya rabamu duk da bambancin da ke tsakaninmu saboda Allah ne Ya halicce mu baki daya,” inji shi.
Alhaji Yaro Makama wanda ya canza sheka daga PDP zuwa APC a watannin baya ya ce gurbin da suka bari a PDP a Jihar Kaduna har yanzu ba a cike shi ba. “Sun kasa cike wannan gurbi da muka bari kuma da yardar Allah sai mun yi sanadin faduwar Jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna tunda dai shegiyar uwa ce mai kashe ’ya’yanta. Ta zama annoba don haka sai mun karasa kashe ta a kasar nan,” inji shi.
Alhaji Makama ya bukaci al’ummar jihar su kasance masu kaunar zaman lafiya a cewarsa babu wata kasa ko al’umma da za ta ci gaba a cikin halin tashin hankali.