Jonathan na kokarin hallaka ni – Kwankwaso
Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya zargi Shugaban kasa, Dokta Goodluck Jonathan da kulla yadda za a hallaka shi a wani sabon babi na takaddamar da ke tsakaninsu.Gwamna Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta musamman da jaridar Premium Times a shekaranjiya Laraba, inda ya ce, Shugaban kasar yana kokarin hallaka […]

Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya zargi Shugaban kasa, Dokta Goodluck Jonathan da kulla yadda za a hallaka shi a wani sabon babi na takaddamar da ke tsakaninsu.
Gwamna Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta musamman da jaridar Premium Times a shekaranjiya Laraba, inda ya ce, Shugaban kasar yana kokarin hallaka shi, har ya bayar da umarnin a janye rabin jami’an tsaronsa a wani yunkuri na bayar da damar a kai masa farmaki.
“Na shaida wa abokaina da jama’ar Jihar Kano da ’yan Najeriya da kuma kasashen duniya su kama Jonathan kan duk abin da ya faru da Kwankwaso ko iyalansa ko kuma jama’ar Jihar Kano,” inji Kwankwaso lokacin da yake bayani a masaukin baki na Gwamnan da ke Abuja.
Ya zargi Shugaban kasa da haddasa wutar rikici a Jihar Kano, bayan da tsohon Gmamnan Babban Bankin Najeriya ya zama Sarkin Kano a ranar Lahadi.
Masu magana da yawun Shugaban kasa, Reuben Abati da Doyin Okupe, ba su mayar da martani ba lokacin da jaridar Premium Times ta tuntube su a shekaranjiyar.
Dangantaka tsakanin Shugaba Jonathan da Gwamna Kwankwaso ta fara tsami ne tun bara, bayan da Kwankwaso ya koma Jam’iyyar APC, kuma tun daga wancan lokaci mutanen biyu suke caccakar juna kan zargin cin hanci da gazawa.
Nada Malam Sanusi Lamido a matsayin Sarkin Kano ne ya sake tado da wutar rikicin, inda PDP da fadar Shugaban kasa suka fito fili suka nuna adawa da takarar tsohon Gwamnan Babban Bankin, wanda Shugaba Jonathan ya kora a watan Fabrairu.
Kwankwaso ya ce yana da “bayani mai tushe’ cewa Shugaban kasar ya umarci magoya bayansa su tayar da ‘kayar baya’ a jihar. “Ba mu san manufarsa ba, amma hakika manufar ba mai kyau ba ce, mun gaya musu tayar da rikici a Jihar Kano ba zai haifar da alheri ga kowa ba. Rikici ya ishe mu a kasar nan, kuma yanzu suna ba magoya bayansu kudi don tayar da zaune-tsaye su kokkone kadarorin gwamnati,” inji shi.
Gwamnan ya zargi Shugaban kasar ta kunna wutar rikici a Jihar Kano, saboda jihar tana karkashin Jam’iyyar APC ne.
“Kwanan nan muka rasa babban Sarki a Gombe, kuma sun bi irin hanyar da muka bi wajen zaben sabon Sarki, amma ba su ce komai ba, saboda jihar PDP ce. Yanzu ga shi suna ba da kudi don a tayar da rikici, ban taba ganin irin wannan abu ba,” inji Kwankwaso.
Gwamna Kwankwaso ya ce sabon Sarkin Kano ya kasa shiga fada ne saboda ’yan sanda sun mamaye fadar, laifin da ya dora shi a wuyan Shugaban kasa. Ya zargi fadar Shugaban kasa da shirya kama Sarkin na Kano don hana nada shi a sarautar, “Mun samu labari suna shirin kama shi, sai muka mayar da shi gidan gwamnati. Ban san abin da zai faru ba da sun samu nasarar yin hakan.
Ya ce yana da goyon bayan jama’ar jihar da kashi 92 cikin 100, kuma abin mamaki ne a ce Shugaban kasa ana haddasa rikici a Kano. Ya ce har yanzu ban san dalilin haka ba, kuma tarihi zai fallasa manufarsu.
Game da mamaye fadar Sarkin Kano, Gwamna Kwankwaso ya ce, gwamnatinsa ta zuba ido domin “ganin iya gudun ruwanmsu.”