Jonathan na wasa da rayuwar ’yan Najeriya – Tsohon Minista

Tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Najeriya, Cif Akin Olujinmi (SAN), ya soki Shugaba Goodluck Jonathan da gaza nuna katabus wajen magance matsalar tsaro da ke addabar kasar nan. Tsohon Ministan wanda yake magana da manema labarai a Osogbo a ranar Talatar da ta gabata, kan kashe dalibai 37 a Jihar Yobe da wani dan […]

Jonathan na wasa da rayuwar ’yan Najeriya – Tsohon Minista
Jonathan na wasa da rayuwar ’yan Najeriya – Tsohon Minista

Tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Najeriya, Cif Akin Olujinmi (SAN), ya soki Shugaba Goodluck Jonathan da gaza nuna katabus wajen magance matsalar tsaro da ke addabar kasar nan.

Tsohon Ministan wanda yake magana da manema labarai a Osogbo a ranar Talatar da ta gabata, kan kashe dalibai 37 a Jihar Yobe da wani dan kunar bakin wake ya yi, ya ce Jonathan yana nuna wa duniya cewa, ya fi damuwa da bukatarsa ta a sake zabensa fiye da magance matsalar tsaro a kasar nan.
Ya ce, “Shugabanninmu ba su mayar da hankali kan abubuwan da suke shafar mafi yawan jama’ar kasar nan, wannan abin takaici ne. Kashe yara ’yan makaranta abin Allah wadai ne, kuma wajibi ne shugabanninmu su mike tsaye su tabbatar akwai cikakken tsaro a kowane bangare na kasar nan.”
Ya kara da cewa “Baya ga daliban da aka kashe ranar Litinin, ’yan matan Chibok da ’yan Boko Haram suka sace suna hannunsu har yanzu babu mai cewa komai a kansu yanzu. Kuma maimakon a tabbatar da an sako ’yan matan sai aka komo ana musguna wa masu kiran a sako su.”
Olujinmi, wanda ya yi minister a zamanin Obasanjo ya soki kaddamar da niyyar takara ta Shugaba Jonathan, inda ya ce duk da cewa zaben 2015 yana da muhimmanci, amma kare kasa ya fi muhimmanci ga masu kaunar kasar nan.
Ya ce an kashe dalibai kuma ba iyayen ’yan matan da aka sace kadai ke jin zafi ba, amma babu mai cewa komai a yanzu. “An fitar da rai ‘’yan matan za su dawo. Ina shawartar Shugaban kasa ya fi mayar da hankali wajen tsaron rayuka da dukiyar ’yan Najeriya. Ba mu taba ganin irin wannan mugun abu a kasar nan ba. Wajibi ne shugabanninmu su yi wani abu,” inji Olujinmi, wanda masanin shari’a ne.