Jonathan ne ya ba ni umarnin kashe kudin da ake zargina -Sanusi
Dakataccen Gwamnar Babban Bankin Najeriya, Malam Sanusi Lamido Sanusi ya amsa tuhumar da aka yi masa na kashe kudi ba bisa ka’ida ba, inda ya bayyana cewa duk kudaden da ake zargin ya kashe Shugaban kasa ne ya umarce shi da ya yi hakan. Ya bayyana hakan ne cikin wata takarda mai shafi 28 da […]

Dakataccen Gwamnar Babban Bankin Najeriya, Malam Sanusi Lamido Sanusi ya amsa tuhumar da aka yi masa na kashe kudi ba bisa ka’ida ba, inda ya bayyana cewa duk kudaden da ake zargin ya kashe Shugaban kasa ne ya umarce shi da ya yi hakan. Ya bayyana hakan ne cikin wata takarda mai shafi 28 da Aminiya ta samu kofi.
Ya bayar da misali da ayyukan tallafawa da Babban Bankin ya yi wadanda rahotan Majalisar Kula da Kudade ta Najeriya(FRCN) ya ce hakan ya saba wa doka. A martaninsa kan wannan, ya ce shugaban kasa ne ya umarce shi da ya biya Naira biliyan 19 da miliyan 700 don sayan jirage masu sulke, masu saukar angulu da kuma wadansu kayayyakin aikin tsaro na Ma’aikatar Harkokin ‘Yan sanda.
Malam Sanusi ya kara da cewa, akwai wani lokaci da Sakataran Gwamnatin Tarayya ya taba rutubo masa bukatar kudi Naira biliyan 2 da milayan 100 don aikin kwaskwariman Zauren Majalisar Zartarwa da ke fadar shugaban kasa. Ya ce bankin bai yi wata-wata ba ya biya wadannan kudade don gudanar da aikin.
Ya kara da cewa, “Bayan wannan akwai kuma wadansu lokuta da Babban Bankin bisa umarnin shugaban kasa ya fara aikin gina Babban Cibiyar Taro ta kasa, Hakazalika, babban bankin ya gina ofis din sabuwar cibiyar nan da ke ba da horo kan dakile ta’addanci wanda ke karkashin ofishin Babban Mai ba Shugaban kasa Shawara ta Fuskar Tsaro, a kan kudi Naira biliyan 3 da miliyan 200“ Inji shi
‘Majalisar Kula da Kudade ta Najeriya(FRCN) ita ma kanta ta amfana da irin wadannan ayyukan da Babban Bankin ya gudanar, domin bankin ya ba ta Naira miliyan 220. Akwai wadansu kuma Naira miliyan 280 wanda muka ba su don daidaita bankuna da ke kan hanyar rugujewa, jimilla Naira miliyan 500 ke nan.’
Da ya komo kan badakalar da ake zargin an yi a Kamfanin Buga Kudi da Muhimman Takardu na kasa (NSPMP) kuwa ya ce an ba kamfanin Naira biliyan 38 da miliyan 233 don buga sababbin takardun kudi. Yadda lissafin yake kuwa shi ne, an fara ba kamfanin ne Naira biliyan 28 da miliyan 738 a shekaran 2011, sai Naira biliyan 6 da miliyan 587 na bashin da ake bin kamfanin da kuma Naira biliyan 2 da miliyan 829 wadanda akayi amfani da su wajen cike gibin kasafin kudin kamfaninin na sherakar 2011.
A kan zargin cewa Babban Bankin ya biya kamfanin jirgin saman na Emirate Airlines Naira miliyan 511 don yin shatar jirgin don zirga-zirgar ma’aikatan babban bankin a cikin Najeriya wanda aka gano cewa kamfanin jirgin ba ya irin wannan aikin. Malam Sanusi ya mai da martani da cewa “Babban Bankin ko da sau daya bai taba shiga wata harka da kamfanin Emirates Airlines ba, ballantana ma har biyan kudi ya shiga.”
Ya ce “Kamfanin Emirates Touch Abiation muke daukar shata duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Amma da Majalisar Kula da Kudade ta Najeriya ta so ta warware duk wadannan zarge-zargen cikin sauki, da ta yi hakan ta hanyar tuntubar kamfanonin da abun ya shafa”
Ya kuma ce wannan gamsasshan lissafin da ya bayar da kuma rubutattun bayanai da yake da su sun isa hujjar da za ta gamsar da shugaban kasa ya sake duba dakatarwar da ya yi masa da idon basira don yi wa batun adalcin da ya dace.
A karshe ya ce zai so shugaban kasa ya waiwayi duk wata hukuma ko ma’aikata ta gwamnatin tarayya da ake wa zargin almundahana don suma su bada gamsasshun bayanai a bayyane da zai wanke su daga duk wani zargi.