Jonathan ne ya tsige Nyako – Kwankwaso

Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi zargin cewa Shugaba Goodluck Jonathan ne ya tsige Gwamnan Jihar Adamawa Murtala Hamman Yero Nyako amma ba ‘yan majalisa ba.Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya yi hira da sashin Hausa na BBC shekaranjiya Laraba.A ranar Talata ne ’yan Majalisar Dokokin Jihar Adamawa suka tsige […]

Jonathan ne ya tsige Nyako – Kwankwaso
Jonathan ne ya tsige Nyako – Kwankwaso

Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi zargin cewa Shugaba Goodluck Jonathan ne ya tsige Gwamnan Jihar Adamawa Murtala Hamman Yero Nyako amma ba ‘yan majalisa ba.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya yi hira da sashin Hausa na BBC shekaranjiya Laraba.
A ranar Talata ne ’yan Majalisar Dokokin Jihar Adamawa suka tsige Nyako inda suka bayyana cewa sun kama shi da laifin cin hanci da rashawa da kuma aikata laifuffukan da suka saba ka’ida.
Ya ce, “A gaskiya wannan abin da ya faru a Jihar Adamawa abin bakin ciki ne kwarai da gaske ga Jihar Adamawa da Najeriya da ma kasashen duniya wadanda suke dimokuradiyya. Abin da ya faru a Jihar Adamawa ya nuna irin kama karya da Jonathan yake yi a wannan kasa tamu Najeriya. Ba ’yan Majalisa ne suka cire Baba Mai Mangwaro ba, na tabbata Jonathan ne ya cire shi.”
Ya ce duk da cewa ’yan majalisa ne suka tsige Nyako amma ya ga hannaye da kafafun Jonathan a cikin shirin tsige Nyako.
“Duk wanda yake sauraren rediyo, ko yake karanta jaridu, ko wanda ya san abin da yake faruwa a Najeriya, ai ya san haka, ba wai mu da muka shiga ciki ba. Na san yadda ’yan majalisar suke, kasancewar na zauna da su, a bisa zaman da na yi da su, na fahimci sa su aka yi.
“Na tabbata idan za a fadi kowane irin laifi, ba za a ce Baba Mai Mangwaro ne ya yi shi kadai ba. Na tabbata an cire shi ne don yana jam’iyyar APC, saboda wadansu dalilan siyasa da aka shigo da su, wadanda ba lallai sai na bayyana su ba. Yanzu babu abin da suke so face a ci mutunci duk wadanda suke APC, wanda hakan ba zai haifar musu da mai ido ba. Wannan abin da ya (Jonathan) yi ba APC kawai ya yi wa ba, ya yi wa kasar nan, ya yi wa dimokuradiyyar duniya. Na tabbata da a ce Baba Mai Mangwaro a PDP yake ba za a tsige shi ba.” Inji Kwankwaso.
Dangane da batun jita-jitar an dauki wannan matakin ne don a ga bayan gwamnonin APC sai ya ce, “jiya wani ya kira ni sai ya ce ga shi a Jihar Nasarawa yana zuga ’yan majalisar jihar don su tsige Al-Makura, a yanzu kuma mun ji sun kai matsayin rubuta takardar zarge-zarge da sauransu.  A baya an kwace Jihar Ekiti, a yanzu an sauke Baba Mai Mangwaro, labarin da muke je ba wai za a cire shi ba ne kawai, a’a, za a hada shi da wadansu don su ci mutuncinsa.
“Tabbas an sako gwamnonin APC a gaba, an kwace Jihar Ekiti, idan ka duba yanzu ga Jihar Nasarawa, sannan ga abin da ya faru a Jihar Edo, ga zaben Jihar Osun na tafe ga sauran wurare da suka sa a gaba, inda suka lashi takobi sai sun sun cim ma nasara. Amma abin da na sani wanda shi (Jonathan) da kuma na kusa da shi ba su sani ba shi ne, wannan shi ne kashe dimokuradiyya layi mikakke.” Inji Kwankwaso.
Ya ce ba zai ce ga matakin da zai dauka ba, kasancewar shi ba shugaban Jam’iyyar APC ba ne, amma ya tabbata shugabannin jam’iyyarsu tana ta kokari irin nata don ganin yadda za a shawo kan al’amarin.
“Ni ba shugaban APC ba ne, amma muna kula da tamu jihar. Kuma abin da na sani a matsayina na Musulmi shi ne, ko APC ba ta yi wani abu ba Allah Zai yi.”
A ranar Talata ce dai ‘yan majalisar jihar Adamawa 18 daga cikin 25 suka tsige Gwamna Murtala Nyako bisa zargin aikata abubuwan da suka saba wa doka. An binciki Gwamnan ne tare da mataimakinsa Bala James Ngilari, amma sa’o’i kadan kafin a tsige su gaba daya sai mataimakin gwamna ya mika wa majalisa takardar ajiye aikinsa, sai aka tsige Nyako shi kadai.
Mika takardar ajiye da mataimakin gwamna ya yi ga majalisa maimakon gwamna ya jawo kace-nace, domin wadansu na ganin murabus din mataimakin gwamnan ba ta yi ba, saboda bai bi ka’ida ba.
Tsige gwamna Nyako bai yi wa ‘yan adawa dadi ba, inda mutane irin su tsohon shugaban Atiku suka shawarci shugaba Jonathan da ya gujin yin amfanin da karfin kujerarsa ta hanyar da ba ta dace ba.
Haka shi ma tsohon gwamnan jihar Kwara Sanata Bukola Saraki ya bayyana tsige gwamna Nyako da aka yi da cewa abin takaici ne.
Manyan lauyoyi da dama suna ganin idan Nyako ya je kotu zai iya samun nasara, domin akwai matsalar a hanyar da aka bi wajen tsige shi. Suka ce irin haka ta taba faruwa da tsohon gwamnan jihar Oyo Rasheed Ladoja, amma da ya je kotu an mayar da shi kujerarsa.
Nyako dai ya ce za shigar da kara a kotu domin a bi masa hakkinsa, kodayake ya ce abin da ya faru da shi kaddara ce daga Allah.
An dai riga an rantsar da shugaban majalisar dokokin jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin gwamna mai riko, wanda zai shirya zaben sabon gwamna a cikin kwana 90.