Jonathan ya aike da sunayen sababbin ministoci

Shugaba Goodluck Jonathan ya aike da sunayen mutum 12 ga Majalisar Dattawa domin neman amincewa ya nada su ministoci. Mutanen sun hada da tsohon mai ba da shawara kan harkokin tsaro, Janar Aliyu Gusau (mai ritaya), daga Zamfara da tsohon Jakadan Najeriya a Ghana, Sanata Musiliu Obanikoro (Legas) da tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Boni Haruna. […]

Jonathan ya aike da sunayen sababbin ministoci
Jonathan ya aike da sunayen sababbin ministoci

Shugaba Goodluck Jonathan ya aike da sunayen mutum 12 ga Majalisar Dattawa domin neman amincewa ya nada su ministoci. Mutanen sun hada da tsohon mai ba da shawara kan harkokin tsaro, Janar Aliyu Gusau (mai ritaya), daga Zamfara da tsohon Jakadan Najeriya a Ghana, Sanata Musiliu Obanikoro (Legas) da tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Boni Haruna. Sauran su ne Muhammad Wakil (Borno) da Alhaji Abduljelili Oyewale Adesiyan (Osun) da Ambasada Aminu Wali (Kano) da Hajiya Jamila Salik (Kano). Sai Akon Etim Eyakenyi (Akwa Ibom) da Lawrencia Labaran Malam (Kaduna) da Dokta T. W. Danagogo (Ribas) da Asabe Asma’u Ahmed (Neja) da Dokta Khaliru Alhassan (Sakkwato). Shugaban kasar ya kuma nada tsohon shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Bamanga Tukur a matsayin shugaban Hukumar Jiragen kasa ta kasa. Tukur wanda tsohon Gwamnan Jihar Bauci Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu, ya maye gurbinsa a ranar Litinin da ta gabata nadinsa na kunshe ne a cikin wata takarda dauke da sanya hannu kakakin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sam Nwaobasi.  Kawu Baraje ne ke rike da mukamin kafin rikicin da ya jawo kafa sabuwar PDP da ta hade da APC a karshen bara.