Jonathan ya barnata kudaden ajiyar Najeriya Dala biliyan 25 – Obasanjo

Tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya zargi Shugaban kasa Goodluck Jonathan da barnata dukiyar ajiyar Najeriya Dala biliyan 25 na rarar man fetur da gwamnatinsa ta bari. Cif Obasanjo ya yi wannan zargi ne lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin mata na shiyyar Kudu maso Yamma a gidansa da ke Abeokuta a ranar Litinin, […]

Jonathan ya barnata kudaden ajiyar Najeriya Dala biliyan 25 – Obasanjo
Jonathan ya barnata kudaden ajiyar Najeriya Dala biliyan 25 – Obasanjo

Tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya zargi Shugaban kasa Goodluck Jonathan da barnata dukiyar ajiyar Najeriya Dala biliyan 25 na rarar man fetur da gwamnatinsa ta bari.

Cif Obasanjo ya yi wannan zargi ne lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin mata na shiyyar Kudu maso Yamma a gidansa da ke Abeokuta a ranar Litinin, inda y ace gwamnatinsa ta bara sama da Dalar Amurka biliyan 25 a nan cikin gida, kuma marigayi Shugaba ’Yar’aduwa ya kara ajiyar zuwa Dala biliyan 35.
Obasanjo ya ce, lokacin da ya sauka daga mulki ya bar Dala Amurka biliyan 40 a Asusun Waje bayan ya biya duk basussukan da ake bin kasar nan, sannan marigayi ’Yar’aduwa ya kara kudin ajiyar zuwa Dala biliyan 60.
Amma a cewar Obasanjo a lokacin Jonathan ajiyar waje ta dawo Dala biliyan 40.
Cif Obasanjo ya bayyana cewa ba wai yana fada da Shugaba Jonathan ba ne ko Jonathan yana fada da shi, a’a ya fi damuwa ne da bukatun kasar nan, don haka bai cika damuwa da masu sukarsa ba.
Ya ce, “Bai kamata tattalin arzikinmu ya lalace haka ba. Lokacin da na sauka daga mulki shekara takwas da ta gabata, na bar dimbin kudi a asusun ajiyarmu bayan mun biya duk basussukanmu. Kimanin Dala biliyan 25 muka ajiye a asusun rarar man fetur. Rarar da aka samu kan kasafi ana ajiye su ne saboda bacin rana…. Amma yau, asusun ya tsiyaye babu abin kirki a ciki.”
Ya ce asusun ajiyar yana da Dala biliyan 40 hade da basusukan da aka yafe mana, sauran bashin bai fi Dala biliyan uku ba. Kuma bayanai sun nuna asusun ajkiyar ya ci gaba da karuwa har zuwa Dala biliyan 67, amma a yau ya ji labarin ajiyar da ta saura ba ta wuce Dala biliyan 30 ba.
Cif Obasanjo ya ce, “Wannan ne ya sa darajar Naira ke dada faduwa game da Dala. Abin zai faru na samu labari idan kana son sayen Dala a yanzu ta kai kusan Naira 192 zuwa 195. Wannan shi ne hakikanin halin da ake ciki. Shin akwai mafia? Akwai, amma ba zai samu nan take ba, domin yana nufin tilas ne mu bar duk munanan ayyukanmu.”
Tun jagorar matan Iyalode ta kasar Yarbawa Misis Lawson ta ce Obasanjo ya zamo wani fitila na haska kasa. “Kai ne kunne da ido a lunguna da sako-sakon Najeriya. Kai ne muryar da dukkan jama’a ke son ji a kan duk wata matsala da ta shafi jama’a. Don haka muna da yakinin muna wurin da ya dace don tattaunawa kan wasu muhimman matsaloli da suke kona mana zukata, domin muna daukarka a matsayin abin dogaro kuma fitilar kasa,” inji ta.
Matan sun ce sun damu da abubuwan da suke faruwa a kasar nan da suke haifar da rashin tsaro da rugujewar tattalin arziki da talauci da almundahana da sauran matsaloli.