Jonathan ya bukaci a cire allunan tallarsa

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan, ya umarci a cire allunan da ke dauke da hotunansa na yakin neman zabe a sassan kasar nan. A wata sanarwa da Mai ba shi shawara a kan hulda da manema labarai ya fitar, Shugaba Jonathan ya umarci dukkan kungiyoyin da suka yi yakin neman zabensa su cire hotunansa a […]

Jonathan ya bukaci a cire allunan tallarsa
Jonathan ya bukaci a cire allunan tallarsa

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan, ya umarci a cire allunan da ke dauke da hotunansa na yakin neman zabe a sassan kasar nan.

A wata sanarwa da Mai ba shi shawara a kan hulda da manema labarai ya fitar, Shugaba Jonathan ya umarci dukkan kungiyoyin da suka yi yakin neman zabensa su cire hotunansa a dukkan wuraren da suka lika su a fadin kasar nan.
Shugaba Jonathan ya ce ya dauki matakin ne domin a tsabtace kasar kafin rantsar da sabon Shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa.
Shugaba Jonathan ya gode wa dukkan mutane da kungiyoyin da suka mara masa baya a yayin da yake yakin neman zabe.