Jonathan ya bukaci ‘yan adawa su fito da mizanin yi wa gwamnatinsa hisabi

Shugaba Jonathan ya kalubalubalanci masu sukar gwamnatinsa da  su fito da kyakkyawan mizanin da za su yi wa gwamnatinsa hisabi da shi. Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da yake gabatar da rahoton gwamnatinsa na tsakiyar wa’adinsa ga ‘yan Najeriya da kuma duniya baki daya.Mista Jonathan ya bukaci a kwatanta ayyukan da ya yi cikin […]

Jonathan ya bukaci ‘yan adawa su fito da mizanin yi wa gwamnatinsa hisabi
Jonathan ya bukaci ‘yan adawa su fito da mizanin yi wa gwamnatinsa hisabi

Shugaba Jonathan ya kalubalubalanci masu sukar gwamnatinsa da  su fito da kyakkyawan mizanin da za su yi wa gwamnatinsa hisabi da shi. Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da yake gabatar da rahoton gwamnatinsa na tsakiyar wa’adinsa ga ‘yan Najeriya da kuma duniya baki daya.
Mista Jonathan ya bukaci a kwatanta ayyukan da ya yi cikin shekara biyu da abubuwan da gwamnatocin da suka gabaci tasa a Najeriya suka gabatar  da kuma sauran shugabannin  nahiyar Afirika.
Ya bukaci wadanda suke sukar gwamnatinsa su fito da tsarin za su gwada ayyukan gwamnatinsa da shi , domin ba zai yiwu a duba takardar  jarabawar dalibi ba sai an yi amfani da wani tsari, ‘’saboda haka ku fito da tsarinku domin ku gwada ayyukanmu.’’ Inji shi.
Kafin shugaban ya gabatar da jawabinsa sai da jami’an gwamnatinsa da suka hada da ministan kudi Ngozi Okonjo-Iweala da ministan tsare-tsare Shamsuddeen Usman, suka yi bayanin nasarorin da gwamnatin Jonathan ta samu a cikin shekara biyu.