Jonathan ya fara yakin neman zabe a fadar sarakuna
Duk da yake saura watanni tara, a fara yakin neman zabubbukan shekarar 2015, kamar yadda jadawalin zaben da Hukumar zabe mai zaman kanta, wato INEC ta fitar a kwanakin baya, amma sai ga shi a ranar Asabar din makon jiya, 15-02-14, Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan, ya fara yakin neman zabensa, daga fadar wasu manya-manyan […]
Duk da yake saura watanni tara, a fara yakin neman zabubbukan shekarar 2015, kamar yadda jadawalin zaben da Hukumar zabe mai zaman kanta, wato INEC ta fitar a kwanakin baya, amma sai ga shi a ranar Asabar din makon jiya, 15-02-14, Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan, ya fara yakin neman zabensa, daga fadar wasu manya-manyan Sarukan gargaji, da masu fada a ji na wasu sassan kasar nan, duk kuwa da an sha jin Shugaba Jonathan, a lokuta da dama ya fada wa `yankasa cewa ba ya son ya karya ka`idojin Hukumar ta INEC, zai jira sai lokaci ya yi.
A waccan rana ta Asabar ba zato, ba tsammani mutanen biraren Kano da Oyo da Ille Ife a cikin jihohin Kano da Oyo da Osun, bi-da-bi suka wayi gari da karbar bakuncin shugaba Jonathancikin garuruwansu, ziyarar da shugaba Jonathan ya yi tabayyanata da cewa ta kashin kansa ce, bata aiki ba, a duk inda ya sauka.
Ba inda jirgin na shugaban kasa ya fara yada zango a waccan rana bayan ya taso daga babban birnin tarayya Abuja, sai birnin Kanon Dabo, inda ya yi wata ganawa ta mintuna 30, da Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero a fadarsa. An ruwaito shugaban kasar, yana cewa wai tunda Mai martaba ya dawo daga jinya a kasar waje yake ta begen ya zo ya duba lafiyarsa, ya kuma gode masa bisa ga kokarinsa na tabbatar da zaman lafiya. “Na dade ina begen in ganka, tun da ka dawo daga jiyya kasar waje. Na yi matukar farin ciki dana sameka cikin koshin lafiya.” In ji Shugaba Jonathan a fadar Sarkin na Kano. Shugaba Jonathan din, ya kuma fada wa Sarkin cewa a kullum a shirye yake ya karbi shawarwari daga Sarakunan gargajiya.
Da yake mayar da martini, Alhaji Ado Bayero, ya nuna godiyarsa ga shugaban kasa a bisa ga ziyarar, sannan sai ya shawarce shi da ya rika tafiya da duk `yan kasar nan cikin gudanar da mulkinsa. “ Ka tafi da kowa da kowa daidai wa daida. Wannan kasa daya ce, kai kuma ne shugabanta. Don haka ka tafiyar da mulkinta ta yadda kowane dan kasa zai yi alfahari da jin shi dan kasa ne,” inji San Kanon, wanda ya kuma nemi shugaban kasar da ya kara mayar da hankali wajen ganin garkuwar matakan tsaron kasar nan.
Jirgin na Shugaban Jonathan yana barin Kano, ba inda ya yi burki sai garin Oyo na Jihar Oyo kuma a fadar Alafin na Oyo, Oba Lamidi Oyiwola Adeyemi III, inda suka gana cikin sirri, amma kuma daga bisani Shugaba Jonatahan ya fada wa dimbin mutanen da suka yi dafifi a dakin taron, cewa ziyarar, ta kashin kansa ce, ba ta aiki ba, ya ce ya kuma zo gida ne ya gaida Babansa, don haka ba ya tsammanin wata kalankuwa, duk kuwa da ya cewa ba zai iya kauce mata ba.
A nan Shugaba Jonatahan ya ce ya zo ya gode wa Jihar Oyo da ma al`ummar shiyyar Kudu maso yamma, bisa ga goyon bayan da suka ba shi da jam`iyyarsa a zabubbukan 2015. Inda ya yi fatan abubuwa zasu ci gaba.“Duk daya muke, Ni kuma na kasance naku”, in ji shugaban kasar a fadar Alafin na Oyon.
Kodayake da farko Basaraken na Oyo ya so ya noke, yana mai cewa tunda shugaban kasa ya ki ya ce kome illa ya bayyana ziyarar ta kashin kai, to, shi ma ba zai ce kome ba, amma kuma daga baya, ya fadi cewa shugaban kasa ya neme shi ne da sauranSarakunan kasar nan, da su tabbatar da jama`arsu na zaune cikin kwanciyar hankali da junansu.
A can fadar Ooni na Ife Oba Sijiwade Okunade da ke Ille Ife kuwa, inda can shugaban kasar ya zarce a dai ranar ta Asabat din makon jiyan, can ma ganawar sirri suka yi ita ma ta kusan tsawon mintuna 30, amma wata majiya mai tushe ta fadar, ta fada wa manema labarai cewa ganawar shugabannin biyu an yi ta ne bisa bukatar Shugaba Jonatahan, kuma ta dogara ne kacokan akan irin yadda Shugaba Jonatahan zai samu goyon bayan al`ummarYarbawa a zabubbukan 2015. Dukkan wadannan manya-manyanSarakuna uku da Shugaba Jonatahan ya gana da su, bayan kasancewarsu shugabannin Majalisun Sarukan jihohinsu, suna kuma cikin Sarakuna masu fada a ji, ba wai a jihohinsu kawai ba, a`a, har ma da kasa baki daya.
Mai karatu ka ji wasu daga cikin irin yadda abubuwa suka wakana a waccan ziyara ta Shugaba Jonatahan, ziyarar da masukula da abubuwan da ka je su komo na harkokin siyasar kasar nan suka ce yanzu Shugaba Jonatahan ya fara wannan ziyara,wadda tabbas bayan ya kammala da Sarakuna zai kuma waiwayi duk wani mai fada a ji na kasar nan da aniyar neman samun goyon bayansu.
Amma babban abin la`akari ga wadanda aka fara kaiwa ko wadanda za a kaima irin wannan ziyarar neman goyon bayansu, bai wuce su yi amfani da isharar da ta faru a zabubbukan shekarar 2011, inda aka rika bin gidajen wasu daga cikin irin wadancan mutane ana konawa. Don haka ga Sarakunanmu da masu fada aji, ya kamata a wannan karon su yi nesa-nesa da harkokin siyasar kasar nan, muddin suna son su ceci kimarsu da mutuncinsu ga mutanensu, abin da idan ba su yi ba, to, su saurari irin yadda za su kwashe da talakawansu a zabubbukan 2015 din da ma na gaba, don kuwa siyasar wannan jamhuriyar ba irin ta jamhuriyar farko ba ce, da Sarukana da masu fada aji ke yin yadda suke so, su kwana jafiya. Allah Ya kiyaye.
Ni a tawa wautar koda wasu Sarakunan gargajiya na tunanin ta sanadin wasu `yan siyasa suka zo kan karagar mulki, kuma suna jin tsoron kar su raba su da mulki, to, bai kamata su rika mika wuyansu ga masu mulkin siyasar wannan zamanin ba, suna watsi da abin takawansu suke bukata ba. Tabbas, yin hakan ba abin da zai kara jefa su a rayuwa sai kaskanci.
Ga Shugaba Jonatahan ya kamata ya sa ni cewa idan ya bi Sarukana ko ina ya samu goyon baya, Sarakunan kasar Yarbawa, ba za su bishi ba, don kuwa su siyasarsu tamfar kungiyar asiri ce, wadda in suka taru suka ce a yi kaza, za ka ga cewa mafi yawansu can za su yi,haka tarihin zamantakewarsu a kasar nan ya tabbatar tun tuni batun yau ba. Mu dai Allah Ya ba mu ikon zaben shugabanni nagari, amin summa amin.