Jonathan ya fusata saboda rashin daukar nauyin Kiristoci masu ziyara a Arewa
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya zargi wasu gwamnonin Arewa maso Yamma da suka hada da Sakkwato da Zamfara da Kebbi da Kano da Jigawa da Kaduna kan tauye Kiristoci a jihohinsu ta hanyar gaza daukar nauyinsu zuwa ziyarar bauta a Urshalima.Jaridar Premium Times da ke fitowa a Intanet ce ta ruwaito haka a ranar […]

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya zargi wasu gwamnonin Arewa maso Yamma da suka hada da Sakkwato da Zamfara da Kebbi da Kano da Jigawa da Kaduna kan tauye Kiristoci a jihohinsu ta hanyar gaza daukar nauyinsu zuwa ziyarar bauta a Urshalima.
Jaridar Premium Times da ke fitowa a Intanet ce ta ruwaito haka a ranar Talata, inda ta ce Shugaba Jonathan ya bayyana haka ne ga wakilan Majalisar koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, a karkashin Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ada Abubakar, yayin da ta ziyarce shi domin koka masa kan yadda aka tauye Musulmi a wakilcin taron kasa da ake gudanarwa a Abuja.
Jaridar ta ce bayan mayar da bayani game da korafin danne Musulmin Najeriya a wurin taron ne, sai Shugaban kasar ya ba maziyartan mamaki, inda ya ce yana da nasa korafin kan wasu shugabannin Musulmi daga Arewa maso Yamma.
“Har yanzu na kasa gane abin da ya sa gwamnoni, musamman daga Arewa maso Yamma, ba su son daukar nauyin Kiristoci zuwa ziyarar bauta a Urshalima,” kamar yadda aka ruwaito Shugaban kasar yana cewa.
Ya kara da cewa: “Idan ka dauki nauyin Musulmi zuwa Makka, sai ka dauki nauyin Kirista zuwa Urshalima. Idan ba ka yi haka ba, ka tauyye wani ke nan, kuma wannan rashin adalci ne ga Kiristoci.”
Jaridar ta ce Shugaban kasar ya shaida wa bakin nasa da suka hada da Babban Sakataren Majalisar, Dokta Isiak Oloyode cewa lokacin da yake Gwamna a Jihar Bayelsa da ke Kudu maso Kudu yana yawan daukar nauyin Musulmi, wadanda su ne marasa rinjaye a jihar zuwa Makka. Don haka sai ya bukaci Sarkin Musulmi da sauran wakilan su taimaka wajen matsa wa gwamnonin su guji nuna kowace irin danniyar addini.
Jaridar ta ce a watan Maris din bara ma sai da Shugaba Jonathan ya nuna irin wannan damuwa lokacin da ya karbi bakunci shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya kuma jagoran ayarin Najeriya zuwa ziyara a Urshalima na shekarar 2012 a fadar Shugaban kasar.
Wannan mataki na Shugaban kasa ya zo ne a daidai lokacin da ’yan Najeriya suke neman gwamnatoci su daina daukar kudin talakawa suna tura jama’a aikin Hajji ko zuwa Urshalima. Kuma wani kwamiti da ya kafa, a karkashin Orosanye, ya bukace shi ya rusa hukumomin Aikin Hajji da na masu ziyarar Urshalima.
A kwanakin baya ma Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce jihar ta yi tsimin Naira biliyan daya sakamakon shawarar da ta yanke na daina daukar nauyin mutane zuwa aikin Hajji. Gwamnan, wanda ya bayyana haka a wurin Laccar Tunawa da Malam Aminu Kano karo na 30, ya ce an sarrafa kudin wajen ayyukan inganta ilimi da sufuri da kiwon lafiya. Kwankwaso ya fadi a wurin taron cewa: “Babu inda Musulunci ya amince a dauki kudin jama’a a biya wa wasu daidaikun mutane kudin aikin Hajji.”
Wata majiya a wurin ganawar majalisar da Jonathan ta ce, “Mun kadu lokacin da Shugaban kasar ya jingine batun da ya kai mu ya koma yana magana a kan batun daukar nauyin masu ziyara zuwa Urshalima.”
Wata majiyar fadar Shugaban kasar ta shaida wa jaridar cewa a ganawar dai Sarkin Musulmi ya shaida wa Shugaban kasar cewa a matsayinsa na jagoran Musulmi yana samun matsi daga sassa da dama kan yadda aka danne Musulmi a wakilcin taron kasar.
Ya shaida masa cewa Musulmi sun kai wuya kan wannan lamari don haka akwai bukatar Shugaban kasar ya gaggauta daukar mataki kan lamarin don kwantar da kurar da ke neman tashi.