… Jonathan ya gaza – kungiyar CAN

kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), resehen jihohin Arewa ta Tsakiya ta bukaci Majalisar dinkin Duniya ta kawo wa Najeriya dauki domin ceto ta a fafata yaki da maharan Boko Haram da take yi, inda ta ce gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan ta gaza wajen magance tashe-tashen hankulan da Boko Haram ke haddawa a shekara biyar a […]

… Jonathan ya gaza – kungiyar CAN
… Jonathan ya gaza – kungiyar CAN

kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), resehen jihohin Arewa ta Tsakiya ta bukaci Majalisar dinkin Duniya ta kawo wa Najeriya dauki domin ceto ta a fafata yaki da maharan Boko Haram da take yi, inda ta ce gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan ta gaza wajen magance tashe-tashen hankulan da Boko Haram ke haddawa a shekara biyar a yankin Arewa maso Gabas.

Wakilin kungiyar CAN na shiyyar wadanda suka bayyana rashin jin dadinsu da gwamnatin Jonathan bayan wani taro da suka gudanar a Jos fadar Jihar Filato sun ce, “Tunda Najeriya a matsayinta na kasa ba za ta iya kawo karshen tu’annatin mayakan Boko Haram ba, ya zama wajibi a kanmu mu yi kira da babbar murya ga Majalisar dinkin Duniya ta kawo mana dauki, saboda gwamnatin Goodluck Jonathan ta yi matukar gazawa.”
Taron ya samu halartar wakilan kungiyar CAN daga jihohi shida na Arewa ta Tsakiya, inda Daniel Kaze, Mataimakin Shugaban kungiyar CAN na Shiyyar Arewa ta Tsakiya ya ce, “Gwamnatin Shugaba Jonathan ta gaza kare mu, kuma a fili yake kasar nan ba za ta iya maganace matsalar Boko Haram ba.”

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi