Jonathan ya kaddamar da gonar shinkafa mafi girma a Najeriya
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya kaddamar da gonar shinkafa mafi girma a Najeriya da ake kira Olam Farm a kauyen Rukubi da ke Jihar Nasarawa, inda ya yaba wa gwamnatin jihar kan goyon bayan da ta bayar wajen tabbatar da gonar ta fara aiki a jihar. Shugaba Jonathan ya ce gwamnatinsa za ta ba […]
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya kaddamar da gonar shinkafa mafi girma a Najeriya da ake kira Olam Farm a kauyen Rukubi da ke Jihar Nasarawa, inda ya yaba wa gwamnatin jihar kan goyon bayan da ta bayar wajen tabbatar da gonar ta fara aiki a jihar. Shugaba Jonathan ya ce gwamnatinsa za ta ba jihar fifiko a wannan fanni don bunkasa ta, inda ya ce wannan karamci zai rage yawan kudin da ake kashewa wajen shigo da shinkafa cikin kasar nan.
Ya ce nan da shekara biyar masu zuwa kasar nan za ta kasance daya daga cikin kasashen da suka fi fitar da shinkafa a duniya.
Tun farko a jawabinsa Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura ya jinjina wa hukumar gudanarwar gonar shinkafar dangane da saka jari a jihar, inda ya ce shirin na daya daga cikin hanyoyin kirkiro da aikin yi ga al’ummar jihar da kasa baki daya da kuma tabbatar da ci gaba mai dorewa.
Ya yaba kyakkyawar hadin gwiwa a tsakanin gwamnatinsa da kamfanin na kasar Singapore a bangaren sarrafa shinkafa da sauransu. Ya ce wasu bangarori da gwamnatin jihar za ta hada kai da Singapore sun hada da bunkasa ilimin kere-kere da sauransu. Ministan Gona Mista Akinyomi Adeshina ya ce kasar nan a cikin ’yan shekaru da suka gabata an samu dimbin nasarori a bangaren fasaha, a cewarsa tsare-tsare da Gwamnatin Tarayya ke yi musamman a bangaren noma suna haifar da da mai ido.
A nasu bangaren shugaban gonar na Nahiyar Afirka, Benka Frameni da shugaban gonar na kasar nan Mukul Badul sun yaba wa wadanda suka taimaka wajen kafuwar gonar, sun ce sun dauki matakin sadaukar da gonar ce ga ’yan Najeriya don taimaka musu da abinci. Taron ya samu halartar gwamnonin jihohin Benuwai Gabriel Suswan da na Kogi Idris Wada da wakilin Gwamnan Jihar Neja da Ministan Ciniki da Saka Jari Olushegun Aganga da takwararsa na Labarai Mista Labaran Maku da na Albarkatun Ruwa Sarah Ochikpe.