Jonathan ya kai wa Buhari ziyarar godiya

Kammala aikin jirgin kasa ya nuna Buhari bai watsar da ayyukan gwamnatocin baya ba, inji Jonathan.

Jonathan ya kai wa Buhari ziyarar godiya

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan a lokacin wata ziyara da ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari a Fadar Shugaban Kasa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa da tsohon Shugaban Kasa Goodluck a ranar Talata 21 ga watan Yuli.

Jonathan wanda ziyarsa ta zo bayan a ranar Asabar Shugaba Buhari ya sanya sunansa, Goodluck Jonathan, a tashar jirgin kasa ta Agbor, ya yaba wa Buhari kan kammala ayyukan da gwamnatocin baya suka fara.

“Ina amfani da wannan dama wajen jinjina wa Shugaban Kasa a bainar jama’a, duk da cewa na aika masa da wasikar godiya.Abu mai kyau ne. Kazalika kammala aikin jirgin kasan ya tabbatar da cewa shugaban kasa ya ci gaba da ayyukan da gwamnatocin baya suka fara ba, wanda shi ne abin da ya kamata a rika ka yi”, inji shi.

Ya shaida wa ’yan jarida Fadar Shugaban Kasa cewa akwai kyakkyawar danganka a tsakaninsu kuma zai ci gaba da kawo masa ziyara.

Tashar jirgi ta Goodluck Jonathan da ke Agbor, ita ce mafi girma a layin jirgi da ya tashi daga Itakpe a jihar Kogi zuwa Sapele a Warri a Jihar Delta.