Jonathan ya kasa gabatar da kasafi ga majalisa

A karo na biyu Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya kasa gabatar da kasafin kudin badi ga zaman hadaka na Majalisar Tarayya. Shugaban ya bukaci ya gabatar da kasafin a ranar 12 ga Nuwamba, amma ya gaza bisa fargabar da yake yi na wasu ’yan Majalisar Wakilai daga Jam’iyyar PDP da ta rabu biyu sun […]

Jonathan ya kasa gabatar da kasafi ga majalisa

Shugaba Goodluck JonathanA karo na biyu Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya kasa gabatar da kasafin kudin badi ga zaman hadaka na Majalisar Tarayya. Shugaban ya bukaci ya gabatar da kasafin a ranar 12 ga Nuwamba, amma ya gaza bisa fargabar da yake yi na wasu ’yan Majalisar Wakilai daga Jam’iyyar PDP da ta rabu biyu sun shirya wargaza zaman, don haka ya tura gabatarwa zuwa ranar Talatar da ta gabata, amma saura awa uku ya je majalisar ya sake dage zuwan.
A wata wasika da ya aike ga zaurukan majalisar biyu Shugaba Jonathan ya ce ba zai gabatar da kasafin ba ne saboda ’yan majalisar suna da sabani kan kudin man fetur da kasafin ya fi dogara a kai. Sai dai ’yan majalisa da dama sun yi watsi da wannan hujja, inda suka ce irin wannan matsala ba ta hana shi gabatar da kasafi ba a baya ba.
Alamu sun nuna Shugaban ba zai je majalisar ba ce da rana, bayan an shirya tsaf don karbarsa. Alama ta farko ita ce ana cikin jira aka zo aka dauke kujerar Shugaban Majalisar Dattawa, sannan a Shugaban Majalisar Wakilai, sai kujerun ministoci da manyan jami’ai daga zauren majalisar. Sannan aka nemi ma’aikata aka rasa a ginin majalisar, yayin da jami’an tsaro da suka karkasu a cikin zauren suka fara ficewa inda cikin mintoci aka neme su aka rasa. Wannan ya nuna cewa babban bakon da ake sa ran zuwansa ba zai zo ba.
Labari na watsuwa kan halin da ake ciki kananan ma’aikata da aka hana zuwa aiki kafin karfe 2:00 na rana suka fara bayyana, yayin da sanatoci da wakilai suka koma kan harkokinsu nay au da kullum.  
Wasikar Jonathan ta dora rashin gabatar da kasafin kan sabanin kudin mai kan kowace ganga, inda sanatoci suka ajiye kan Dala 76 da rabi su kuma wakilai suka ajiye kan Dala 79, inda ya ce ya dage gabatar da kasafin sai zaurukan majalisar sun daidaita kansu kan haka.
Majiyarmu ta ce ’ya’yan sabuwar PDP sun sha alwashin gwasale Jonathan yayin gabatar da kasafin, sakamakon yadda aka gwasale musu shugabansu Kawu Baraje lokacin da ya ziyarci majalisar a watannin baya. Majiyar ta ce an shafe kwanakin karshen mako ana taro don lallashin ’yan sabuwar PDP ba tare da nasarar kirki ba, wadanda suka ce sai wadanda suka wulakanta shugabansu sun tura masu neman gafara ga jagorar Gwamnonin G7 kuma sun nemi gafara a zauren majalisar kafin su mayar da wukakensu.
Sai dai mashawarcin Shugaban kasa kan harkokin siyasa Ahmed Gulak ya ce babu kanshin gaskiya kan Shugaban ya kasa gabatar da kasafin ne saboda tsoron gwasale shi a majalisar.