Jonathan ya ki karbar shugabancin Kwamitin Dattawan PDP

Shugaban kasa mai barin gado a yau, Dokta Goodluck Jonathan ya ki karbar shugabancin Kwamitin Dattawan Jam’iyyar PDP. Shugaban kwamitin Tony Anenih wanda ya sauka daga shugabancin kwamitin a makon jiya ya ce ya sauka ne domin ba Jonathan damar zama shugaban kwamitin, sai dai kuma Jonathan ya ki amincewa ya karbi mukamin a wajen […]

Jonathan ya ki karbar shugabancin Kwamitin Dattawan PDP
Jonathan ya ki karbar shugabancin Kwamitin Dattawan PDP

Shugaban kasa mai barin gado a yau, Dokta Goodluck Jonathan ya ki karbar shugabancin Kwamitin Dattawan Jam’iyyar PDP.

Shugaban kwamitin Tony Anenih wanda ya sauka daga shugabancin kwamitin a makon jiya ya ce ya sauka ne domin ba Jonathan damar zama shugaban kwamitin, sai dai kuma Jonathan ya ki amincewa ya karbi mukamin a wajen wani taron da aka gudanar a fadar Shugaban kasa a ranar Litinin da ta gabata.
Da yake yi wa manema bayani bayan taron Sakataren Kwamitin Sanata Walid Jibrin, ya ce Jonathan ya ki amincewa da karbar mukamin, ya ce wannan ya sa kwamitin ya nada tsohon mukaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Bello Halliru a matsayin shugaban riko na kwamitin.
Ya ce Bello zai riko kuejrar ce na tsawon wata biyu zuwa uku lokacin da za a zabi shugaban kwamitin dattawan jam’iyyar. Bayanai sun ce sunan Bello Halliru kawai aka gabatar don rike mukamin a lokacin taron.
BelloHalliru wanda tsohon Ministan Tsaro ne daga baya ya shaida wa manema labarai cewa aikinsa shi ne ya sake fasalin PDP domin mayar da ita ta ci gaba da zama babbar jam’iyyar siyasa a Afirka.
Taron wanda aka fara shi da karfe 9:07 na dare an kare shi da misalin karfe 11:00 na dare, kuma cikin wadanda suka halaci taron akwai Anenih da mukaddashin Shugaban PDP na kasa, Uche Secondus da Mataimakin Shugaban kasa mai baring ado Namadi Sambo da Shugaban Majalisar Dattawa Dabid Mark da mataimamkinsa Ike Ekweremadu da Sanata Walid Jibril da Farfesa Jerry Gana da Shugabar Mata ta PDP, Kema Chikwe da Bello Haliru da kuma tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Nasiru Ibrahim Mantu.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Ahmed Mohammed Makarfi da tsohuwar Ministar Mata, Josephine Anenih da Shugaban Ma’aikata na Jonathan, Jones Arogbofa da Sanata Hope Uzodinma.
A ranar Larabar makon jiya ne Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Ahmadu Adamu Mu’azu ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar, yna ma bayyana rashin koshin lafiya a matsayin dalilin saukarsa; yayin da Anenih ya biyo baya a ranar yana mai cewa ya yi haka ne don ba Jonathan damar karabar shugabancin Kwamitin Dattawan Jam’iyyar idan wa’adinsa na mulki ya kare a yau.