Jonathan ya kori Janar Agwai saboda halartar taron Obasanjo

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya kori Janar Martin-Luther Agwai daga shugabancin Asusun karin Kudin Man Fetur, (SURE-P). Janar Agwai Babban Hafsan Tsaro ne da ake girmamawa da ya jagoranci Rundunar Sojin Majalisar dinkin Duniya a kasar Sudan da sauran ayyukan soja da dama. Shugaba Jonathan ya nada Janar Agwai a matsayin Shugaban SURE-P wani […]

Jonathan ya kori Janar Agwai saboda halartar taron Obasanjo
Jonathan ya kori Janar Agwai saboda halartar taron Obasanjo

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya kori Janar Martin-Luther Agwai daga shugabancin Asusun karin Kudin Man Fetur, (SURE-P).

Janar Agwai Babban Hafsan Tsaro ne da ake girmamawa da ya jagoranci Rundunar Sojin Majalisar dinkin Duniya a kasar Sudan da sauran ayyukan soja da dama. Shugaba Jonathan ya nada Janar Agwai a matsayin Shugaban SURE-P wani bangare da gwamnati ta kirkiro don rarraba kudin da aka tara daga janye tallafin man fetur don samar da kayan more rayuwa da aikin yi.
Kakakin Shugaban kasa Reuben Abati ya ce a ranar Talata, Shugaba Jonathan ya nada Ishaya Dare Akau a matsayin sabon shugaban shirin SURE-P. Sabon Shugaban SURE-P din ya fito ne daga karamar Hukumar Jema’a da ke Jihar Kaduna, kuma yana da Digiri a fannin fasaha da wani a fannin shari’a.
Mista Akau tsohon ma’aikacin gwamnati ne da ya taba zama Shugaban Hukumar UBE ta Jihar Kaduna da kuma Hukumar Harkokin Majalisar Tarayya.
Duk da fadar Shugaban kasa ba ta bayyana dalilan cire Janar Agwai ba, Jaridar Premium Times ta ce ta samu labarin cewa an kori Janar Agwai ne saboda ya keta umarnin Shugaban kasa na kada wani jami’in gwamnati ko dan Jam’iyyar PDP ya halarci bikin taya tsohon Shugaba kasa Obasanjo murnar ranar haihuwarsa a makon jiya. Dangantaka tsakanin Jonathan da Obasanjo ta yi tsami inda a makon jiya Obasanjo ya kekketa katin zama dan Jam’iyyar PDP, don nuna ficewarsa daga jam’iyyar.
Jaridar ta ce, lokacin da aka sanar da Janar Agwai wanda a zamanin Obasanjo ne shahararsa ta bayyana umranin na Jonathan, ya ce zai halarci bikin, inda kuma ya gabatar da laccar da a ciki ya ce tilas ne shugabannin su zauna da shirin za a iya bukatar canji a kowane lokaci.
Janar Agwai ya maye gurbin Cif Christopher Kolade ne, wanda ya bar mukamin bayan ya soki Shugaba Jonathan.
A baya-bayan nan an samu zargin cewa an samu sabanin tsakanin Janar Agwai da gwamnati kan asusun SURE-P, inda aka ce Janar din ya ki a yi amfani da kudin SURE-P don yi wa Jonathan kamfe.
Masu zargin sun ce wasu daga cikin ko’odinitocin kamfe din Jonathan a zaben 2011 su ne ko’odinitocin shirin SURE-P a wasu jihohin kasar nan a yanzu wadanda suka hada da Alhaji Bode Oyedele, (Legas) da Mitsa Joseph Ishekpa (Nasarawa) da Alhaji Garba A. Kurfi (Katsina) da Alhaji Aliyu Mamman (Neja) da Alhaji Adamu Yaro Gombe (Gombe) da Femi Akinyemi (Ekiti) da Jarigbe Agbom Jarigbe (Kuros Riba) da Cif Abdullahi Ohioma (Kogi) da Dare Adeleke (Oyo) da Alhaji Al-kasim Madoka (Kano) da kuma Alhaji Kolo Bukar (Borno).