Jonathan ya mayar da Babban Bankin Najeriya kamar ATM – Soludo

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya Farfesa Charles Soludo, ya ce tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya rika gudanar da bankin ne kamar wani fim na yadda kasar Uganda take a karkashin Idi Amin.Marigayi Idi-Amin Dada ya mulki kasar Uganda ne a tsakanin 1971 da 1979 kuma ana bayyana shi a matsayin mafi almundahana a tsakanin […]

Jonathan ya mayar da Babban Bankin Najeriya kamar ATM – Soludo
Jonathan ya mayar da Babban Bankin Najeriya kamar ATM – Soludo

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya Farfesa Charles Soludo, ya ce tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya rika gudanar da bankin ne kamar wani fim na yadda kasar Uganda take a karkashin Idi Amin.
Marigayi Idi-Amin Dada ya mulki kasar Uganda ne a tsakanin 1971 da 1979 kuma ana bayyana shi a matsayin mafi almundahana a tsakanin shugabannin Afirka.
Farfesa Soludo ya ce: “Abin mamaki kamar wasan kwaikwayo a ce Shugaban kasa yana ba Babban Bankin Najeriya umarnin ya kirkiro wani asusun tallafi domin tabbatar da daidaituwar al’amuran kasa kuma Babban Bankin ya ‘buga’ misalin Naira tiriliyan uku a dauki tsabar kudin ya ba fadar Shugaban kasa don gudanar da kamfen ko yin wani abu da ya ga dama, wannan abin takaici ne.”
Farfesa Soludo ya ci gaba da cewa: “Mun tunkari wani mummunan hadari a fannin tattalin arziki. Ban san wata kasa da ta yi haka ba, sai dai abin da na gani a wani fim kan Idi Amin da Gwamnan Babban Bankinsa.”
Farfesa Soludo ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ta fito a mujallar The Interbiew, inda tsohon Gwamnan Babban Bankin ya bayyana bankin da “Na’urar cirar kudi,” a karkashin Jonathan.
Ya ce abin takaici ne duk da cewa bankin yana da ’yancin gashin kansa, amma yana ci gaba da zama bi-ta-zaizai a hannun manyan ’yan siyasa wadanda galibi ‘suke juya akalar’ shugabannin bankin.
Farfesa Soludo ya ce “fallasar baya-bayan nan game da ‘badakalar sayo makamai’ (ta Dala biliyan 2.1 da ta shafi tsohon Mashawarcin Shugaban kasa kanTsaro Sambo Dasuki) da kuma yadda aka tozarta Babban Bankin ya koma kamar na’urar cirar kudi ta fadar Shugaban kasa ya kamata ya sanya mutane tunani a kai.”
Tsohon Gwamnan Babban Bankin yana daga cikin masana tattalin arziki da ’yan kasuwa da aka tattauna da su a bugun mujallar ta The Interbiew na bayan nan, inda suka tattauna kan dama da kalubalen da tattalin arziki zai fuskanta a bana, kama daga sana’anta kayayyaki da batun wutar lantarki da harkokin banki da zuba jari da kananan harkokin kasuwanci da tallace-tallace da samar da aikin yi.
Shugaban kungiyar masu Masana’antu ta Najeriya (MAN) Mista Frank Jacobs, ya bayyana takaita harkar canji kudi da rashin kayayyakin aiki da tsadar harkokin rayuwa a matsayin manyan matsaloli uku da suke kawo barazana ga tattalin arziki. Sai ya ba da shawarar a guji kara kudin haraji, maimakon haka a inganta hanyar karbo harajin tare da hana karkatar da su.