Jonathan ya musanta zargin da Osinbajo ya masa

Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya musanta zargiin da Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi cewa gwamnatinsa ta barnata Naira biliyan 100 da wasu Dala miliyan 289 gab da zaben 2015. Mai taimaka wa tsohon Shugaban kasar kan Harkokin Watsa Labarai, Reno Omokri shi ne ya bayyana haka a wata takarda da ya raba […]

Jonathan ya musanta zargin da Osinbajo ya masa


Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya musanta zargiin da Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi cewa gwamnatinsa ta barnata Naira biliyan 100 da wasu Dala miliyan 289 gab da zaben 2015.

Mai taimaka wa tsohon Shugaban kasar kan Harkokin Watsa Labarai, Reno Omokri shi ne ya bayyana haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai, inda ya ce idan har abin da Osinbajo ya fadi gaskiya ne, to ya tabbatar wa duniya cewa gaske ne ta hanyar bayyana hujjojin da za su tabbatar da zargin nasa. Takardar ta ci gaba da cewa, “Ba wannan ne karo na farko da Osinbajo yake furta irin wannan zargi ba. Kuma ya bari Shaidan yana tasiri a zantukansa, domin kuwa maganganun nasa ba su da tushe balle makama.” 

“Bari in gaya muku gaskiya, Jonathan bai kashe Naira biliyan 150 ba makonni biyu kafin zabe, idan kuma akwai shaidar ya yi hakan, to a baza ta a faifai kowa ya gani. Sannan ba gaskiya ba ce cewa da ya yi wai Jonathan ya kashe  Naira biliyan 14 domin bunkasa ayyukan noma a kasar nan cikin shekara uku. Amma a sarari yake cewa Gwamnatin Buhari da ba ta wuce shekara uku kan mulki ba, ta ciwo bashin da PDP ba ta ciwo ba a tsawon shekara 16 da ta yi tana mulki,” a cewar takardar.

A farkon wannan mako ne Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Gwamnatin  Goodluck Jonathan ta barnata Naira biliyan 150, makonni biyu kafin babban zaben da ya gabata a shekarar 2015.