Jonathan ya nada Mista Osita Chidoka Ministan Sufurin Jiragen Sama
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya nada tsohon Shugaban Hukumar Kiyaye Haddura ta kasa (FRSC) Mista Osita Chidoka, a matsayin sabon Ministan Sufurin Jiragen Sama.Mista Chidoka an rantsar da shi ne shekaranjiya Laraba tare da Malam Abubakar Olanrewaju wanda aka nada Ministan Tsare-Tsare na kasa.Abubakar Olanrewaju wanda ya fito daga Jihar Kwara ya maye gurbin […]
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya nada tsohon Shugaban Hukumar Kiyaye Haddura ta kasa (FRSC) Mista Osita Chidoka, a matsayin sabon Ministan Sufurin Jiragen Sama.
Mista Chidoka an rantsar da shi ne shekaranjiya Laraba tare da Malam Abubakar Olanrewaju wanda aka nada Ministan Tsare-Tsare na kasa.
Abubakar Olanrewaju wanda ya fito daga Jihar Kwara ya maye gurbin Alhaji Shamsudeen Usman, wanda aka sallama a watan Satumban bara. Shi kuma Chidoka ya maye gurbin Misis Stella Oduah ce wadda aka kora a wkatan Fabrairun bana sakamakon zarge-zargen cin hanci da almundahana.
Kafin nada Olanrewaju Minista a Ma’aikatar Kudi Alhaji Bashir Yuguda ne ke kula da Ma’aikatar Tsare-Tsaren.
Ministocin biyu an rantsar da su kafin fara taron Majalisar Zartarwa ta kasa da ke yi kowace Laraba.
dan asalin Jihar Anambra, Mista Chidoka ya haye kujerar Minista ne bayan rigimar siyasa a jiharsa ta tilasta Shugaba Jonathan sauya sunan tsohon Gwamnan Jihar Mista Peter Obi wanda da farko ya dauka zai nada a Minista.
Wani babban jigo a Jam’iyar PDP ya ce a matsayinsa na jagoran Jam’iyyar adawa ta APGA da ke mulkin Jihar Anambra, idan aka nada Mista Obi Minista zai bar PDP ta ci gaba da zama marainiya.