Jonathan ya raba kan sarakunan Hausawa a kudu
Alamu na nuni da cewa, Shugaba Goodluck Jonathan ya yi nasarar janyo mummunar baraka a tsakanin sarakunan Hausawan Jihar Legas inda majalisar sarkin Hausawan Agege ta futo karara ta nisanta kanta daga furucin da aka ce sarki Kabiru ya yi na yi wa Jonathan mubaya’a. Da yake magana a madadin majalisar sarkin Hausawan Agege, Sardaunan […]
Alamu na nuni da cewa, Shugaba Goodluck Jonathan ya yi nasarar janyo mummunar baraka a tsakanin sarakunan Hausawan Jihar Legas inda majalisar sarkin Hausawan Agege ta futo karara ta nisanta kanta daga furucin da aka ce sarki Kabiru ya yi na yi wa Jonathan mubaya’a.
Da yake magana a madadin majalisar sarkin Hausawan Agege, Sardaunan Agege, Alhaji Sani Shu’aibu ya ce majalisar sarkin Hausawan Agege ba ta yi wa shugaba Jonathan ko wani dan takarar jam’iyyar PDP mubaya’a ba kamar yadda sarki Sani Kabiru ya fadi a yayin da ya gana da shugaba Jonathan a Legas a kawanakin baya.
‘Abin da ya faru shi ne shugaba Jonathan ya nemi zai gana da sarakuna amma mafiyawan sarakunan ba su so su gana da shi ba. Daga bisani aka je a matsayinsa na shugaban kasa kuma shugaban kowa da kowa. Da aka je sai shugaban kasa ya ce ya kira su ne don ya ba su hakuri tunda ya hau karagar mulki bai gana da su ba sai yanzu saboda haka su yi hakuri kuma a gaskiya abin da ya kawo shi shi ne yana neman su bashi irin goyon bayan da suka bashi a zaben da ya gabata. Da yake sarki Kabiru shi ne babba kuma shi ne shugaban sarakunan ’yan Arewa da ke Legas sai ya tashi ya ce a gaskiya yallabai a wancan karon mun ba ka goyon baya amma tunda muka zabe ka ba mu kara ganinka ba sai yanzu. Ka na ji idan muka sake baka goyon baya ba za mu sake ganin ka ba kenan? kuma ma tun da muka ba ka goyon baya ba mu fahimci komai ba a gwamnatinka. Mu dai a matsayinmu na sarakuna za mu tabbatar da cewa an yi zabe lafiya kada a yi tashin hankali. Shi kenan sarki ya zauna aka kammala taro kowa ya watse’
Ya ci gaba da cewa ‘Muna tashi kawai sai shugaba Jonathan ya bayar da ummaranin cewa ’yan jaridu da gidan talabijin na NTA su fada cewa Sarakunan ’yan Arewa da ke Legas sun yi masa mubaya’a sun bashi goyon bayan. Da muka ji haka sai muka tara ’yan jaridu a unguwar Surulere muka karyata maganar amma sai mutane suka rika yada jita-jita. Dama haka Jonathan yake yi da ya gana da mutane sai ya kira ’yan jarida ya ce mutanen sun goya masa baya’.
Sarakunan Hausawa da ke jihohi shida na Yammacin kasa sun karyata wani labari da ke cewa, al’ummonin Arewacin kasa mazauna sashen Kudu maso Yamma sun goyi bayan sake zaben Shugaba Goodluck Jonathan a zaben 28 ga watan gobe. Haka kuma sun tabbatar da cewa, ba da yawunsu wasu shugabannin Hausawa suka kai wa Shugaba Goodluck Jonathan ziyara a gidan Gwamnati da ke Marina a Legas cikin makon jiya ba.
A tattaunawar da wakilinmu ya yi da wasu Sarakunan Hausawa da suka nuna kyamarsu ga wannan labari da aka watsa a wasu kafofin yada labarai da sunan bata musu suna. Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad dahiru Zungeru, cewa ya yi “a matsayin Sarkin Hausawan Ibadan kuma Shugaban majalisar sarakunan Hausawan Jihar Oyo, na yi mamakim jin wannan labari da ake cewa gaba dayanmu Sarakunan Hausawa da jama’armu da ke zaune a jihohi shida na Kudu maso Yamma wai mun goyi bayan sake zaben Shugaba Goodluck Jonathan a zabe mai gabatowa. Ba a yi wani zama tare damu a kan wannan magana ba, kuma babu wanda ya gayyace mu zuwa wajen ganawar da Shugaba Jonathan ya yi da wasu mutane da suka ari bakinmu suka ci mana albasa. Saboda haka nake karyata wannan batu domin ba da hannunmu aka saka shi ba.”
“Bayanan da ya iso garemu yana nuna cewa Sarkin Hausawan Ebutte Meta, Legas, Alhaji Sani Kabiru, shi ne ya jagoranci wannan ziyarar ganawa da Shugaba Jonathan a Legas, to, muna ja masa kunne ya daina yin maganganu da yawunmu domin ba mu aike shi ba.” inji shi.
Shi ma Sarkin Kasuwar Alabar Rago, Alhaji Umaru Nagogo Sakkwato, cewa ya yi, “babu wanda ya aike su zuwa ziyarar Shugaba Jonathan, kuma muna karyata batutuwan da suka yi cewa al’ummar Arewa mazauna jihohin Yamma suna goyon bayan sake zaben Jonathan a matsayin Shugaban kasa. Wannan zance ne, karya ce zallanta da wasu ‘yan baranda da suka sayar da mutuncinsu suke yayatawa, domin nuna kwadayinsu a fili. Ba sa daga cikin sahun sanannun shugabanni na al’ummomin ‘yan Arewa.”
Shi kuwa Sarkin Hausawan kasar Egba, Abeokuta, Alhaji Ibrahim Hassan Hassan, cewa ya yi, “a gaskiya na ga sakon gayyata zuwa wajen wannan ganawa da Shugaba Jonathan a Legas, sai dai sakon ya iso cikin kurarren lokaci. Duk da haka na amsa goron gayyata sai dai ba a yi ganawar da ni ba, saboda na yi lattin zuwa. Amma an yi mani bayanin cewa Shugaba Jonathan ya shaida wa taron cewa yana neman goyon bayan a sake zabensa a zabe mai zuwa wanda ban ji dadin wannan bayani ba. Dalili na kuwa shi ne jama’a ta ne suka dora ni bisa wannan matsayi, saboda haka a kowane lokaci ina tare da abin da suke so. Duk da yake ni ba dan siyasa ba ne, amma na lura mafi yawancin jama’ar ‘yan Arewa da ke masarautar Egba, Abeokuta a Jihar Ogun, suna goyon bayan jam’iyyar da ke mulki a jihar ne wato APC saboda haka ina tare da abin da jama’a ta suke so.”
Da aka tuntubi Sarkin Hausawan Ebutte Meta Legas, Alhaji Sani Kabiru, wanda ya jagoranci ganawa da Shugaba Jonathan a Legas, domin jin ta bakinsa sai dai ya yawaita yin alkawari ne ba tare da ya cika ko rubuto sakon waya ba. Har zuwa lokacin rubuta wannan labari Sarki Sani Kabiru bai kira wayar wakilinmu ko aiken sako ba.
Akwai da yawa daga cikin Sarakunan Hausawa dake zaune a wannan sashe, da suka nemi a sakaya sunayensu da suka yi wats da irin wannan zagon kasa da wasu shugabanni suke yi wa jama’arsu domin kwadayin abun duniya. Haka kuma su ma mutane ‘yan Arewa dake zaune a wannan sashe sun mayar da wannan batu abubuwan tattaunawa a wurare daban daban.