Jonathan ya ragargaji Kwankwaso a Kano -Farin jini ya kara mini -Kwankwaso
Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya zargi Gwaman Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da wawure kimanin Naira biliyan 255, wanda aka ware don kananan hukumomi 44 na jihar. Shugaba Jonathan ya yi wanann zargi ne a lokacin da yake jawabi a wajen karbar tsohon Gwaman Kano, Malam Ibrahim Shekarau tare da magoya bayansa cikin Jam’iyyar […]

Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya zargi Gwaman Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da wawure kimanin Naira biliyan 255, wanda aka ware don kananan hukumomi 44 na jihar.
Shugaba Jonathan ya yi wanann zargi ne a lokacin da yake jawabi a wajen karbar tsohon Gwaman Kano, Malam Ibrahim Shekarau tare da magoya bayansa cikin Jam’iyyar PDP.
A cewar shugaban kasar, “Tun daga watan Yunin shekarar 2011 zuwa yau, kananan hukumomin Kano 44 sun samu kudi har Naira biliyan 225, sai dai maimakon Kwankwaso ya kyale su su yi amfani da kudinsu, sai ya karkatar da su ta wata hanyar tare da kashe su yadda ya so, lamarin da ya jawo ake wa shuwagabnnin kanann hukumomin kallon banza”. Inji shi.
Shugaban ya bayyana dalilinsa na kin sanya manyan kayan da aka ba shi a filin jirgi, yana mai nuni da cewa, “Sun ce duk wanda yake sanya hula (malafa) shaidan ne, saboda hakan ne ya sa na ki sanya kayan da aka ba ni (babbar riga) a filin jirgi. Idan ni shaidan ne ta yaya zan yi dukkanin ayyukan da nake yi a Jihar Kano. Tsakanin ni da mutumin da ya handame kudin kananan hukumomi waye shaidanin?”
Da yake bayar da amsa ga jawabin da Gwamna Kwankwaso ya yi a kan da-na-sanin da yake yi game da zaben Jonathan da ya yi a zaben shekarar 2011 kuwa, Shugaba Jonathan ya bayyana cewa, da ma can Kwankwason bai zabe shi ba, sai ma karkatar da kudin yakin neman zabensa da ya yi. “Na karanta a jaridu cewa Kwankwaso yana nadamar kuri’ar da ya jefa mini a lokacin zaben 2011, a iyakar sanina da ma bai zabe ni ba. Abin da ya yi shi ne, ya yi ta shiga da fita tun daga zaben fitar da gwani har zuwa babban zabe, wajen ganin cewa ban kai ga samun nasara ba. A lokacin da ya ga na kusa samun nasara a zaben fidda gwani, sai ya fice daga dakin taron. Muna sane da abin da yake yi, mun dai yi shiru ne kawai.’’
“Ai ko ’yan kudin da muka bayar don a raba wa wakilan da suka zo daga Kano bai ba su ko kwabo ba, saboda ya sanya su ji haushina. Haka kuma kudin da ofis din yakin neman zabena ya ba shi, bai yi amfani da shi yadda ake so ba. Mutumin da ya aikata haka shi ne zai rika gaya wa mutane ya zabe ni a lokacin zabe?” Inji shi.
Shugaba Jonathan ya yi alkwarin karbe kujerar Jihar Kano a zabe mai zuwa. Sannan ya yi alkawarin cewa gwamantinsa na kokarin farfado da dalar gyada a jihar, kamar yadda ya ce, jajircewarsa wajen farfado da ayyukan noma a jihar ta fara haifar da sakamako mai kyau. “Idan kana sanya jar hula ko wani abu na daban ne, to ka sani za mu sake karbe Jihar Kano a zaben 2015.”
Da yake yin Allah wadai da harin bam din da aka kai a garin Abuja, a ranar Litinin, Shugaba Jonathan ya bayyana cewa, “Jihohin da PDP ke mulki suna zaune lafiya lau, wannan ya nuna cewa Jam’iyyar PDP za ta iya samar da zaman lafiya a kasar nan,” Inji shi.
“A shiga Jihar Kano a ga inda kudin suka shiga”
Da yake mai da martani game da zargin da Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi na cewa ya karkatar da kudin kananan hukumomin jihar ta wata hanyar, Gwamnan Kano, Injiniya Rabi’u Kwankwaso ya bayyana cewa ya yi amfani da kudin ne don ciyar da jihar gaba.
Ya mayar da martanin ne a lokacin da yake jawabi yayin bikin rantsar da sababbin daliban Jami’ar North-West karo na biyu.
Gwaman Kwankwaso ya bayyana cewa, idan shugaban kasa yana neman ba’asin yadda aka yi da kudin jihar, to da ya zagaya cikin fadin jihar don gane wa idanunsa ayyukan raya kasa birjik. “Wadansu suna tambayar yadda aka yi da kudin Jihar Kano. Wane kudi suke tambaya? Na shekara hudu ko na shekara takwas? Idan na shekara hudu suke tambaya, to su je Jami’ar North-West, su je Jami’ar Wudil, su je Kwalejin gwamnati, sannan su zaga cikin garin Kano da kananan hukumomi 44 (su gani).” Inji Kwankwaso.
Batun da Gwamna Kwankwaso ya yi na kudin shekaru takwas dai yana nufin shekaru 8 ne na Gwamna Shekarau, wanda ya koma Jam’iyyar PDP.
Gwaman Kwankwaso ya kuma gode wa gwamnonin PDP, wadanda ba su halarci taron na Kano ba, inda ya ce, “Muna gode wa abokanmu gwamnonin PDP da dattijan jam’iyyar da suka ki halartar wanann taro. Wani gwamna ya kira ni ya sanar da ni cewa ba zai halarci taron ba. Mu mun fi su farin jini a jam’iyyar, domin na tabbata ko da yanzu zan yi takarar a jam’iyyar PDP zan ci zabe, don na fi su farin jini”.
Har ila yau Gwamna Kwankwaso ya bayyana cewa, wanann taron da Jam’iyyar PDP ta yi, shi aka yi wa, ganin irin yadda aka rika kiran sunansa a wajen taron, wanda hakan na nufin kara masa farin jini a wajen al’ummar jihar da kasa baki daya.
‘Shiga PDP kamar shiga Musulunci ne’
A jawabiinsa tun farko, Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Ahmad Adamu Mu’azu ya bayyana cewa, shiga Jam’iyyar PDP kamar shiga addinin Musulunci ne. “E, shiga Jam’iyyar PDP kamar shiga addinin Musulunci ne, saboda idan ka karbi Musulunci a yau, to daidai kake da tsofaffin Musulmi da suka dade a cikin addinin, to haka abin yake a jam’iyyarmu ta PDP, idan ka shiga yau, to daidai kake da tsofaffin mambobin jam’iyyar”. Inji shi.
Shi kuwa wanda aka yi taron dominsa, tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya yi alkawarin bauta wa jama’ar jihar tare da yin kira ga Shugaba Jonathan da ya yi kokarin magance matsalar wutar lantarki da ta dade tana damun al’ummar jihar. “Na riga na mika wuya gaba daya don bauta wa al’ummata ba tare da bambancin jam’iyyar da nake ciki ba, matukar dai ina siyasa. Kamata ya yi mu hadu mu taimaki junanmu a matsayin ’yan uwa don kara wa jam’iyya karfi”. Inji shi.
Taron ya samu halartar Mataimakin Shugaban kasa Namadi Sambo da Shugaban Majalisar Dattijai Dabid Mark da Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai Emeka Ihedioha da gwamnonin jihohin Katsina da Kebbi da Akwa Ibom da wadansu ministoci.
Wakilanmu da suka je filin jirgin saman Malam Aminu Kano sun rawaito cewa babu wani wakili daga gwamnatin Jihar Kano da ya je don tarbar Shugaban kasa.