Jonathan ya rantsar da sababbin ministoci
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya rantsar da sababbin ministoci takwas da Majalisar Dattajawa ta tantance a makon jiya tare da tura su ma’aikatun da za su yi aiki. Jim kadan da rantsar da ministocin ne Shugaba Jonathan ya bayyana ma’aikatun da ministocin za su jagoranta.Shugaban ya nada Misis Patricia Akwashiki a matsayin Ministar Watsa […]
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya rantsar da sababbin ministoci takwas da Majalisar Dattajawa ta tantance a makon jiya tare da tura su ma’aikatun da za su yi aiki.
Jim kadan da rantsar da ministocin ne Shugaba Jonathan ya bayyana ma’aikatun da ministocin za su jagoranta.
Shugaban ya nada Misis Patricia Akwashiki a matsayin Ministar Watsa Labarai, yayin da ya nada Farfesa Nicholas Ada Minista a Ma’aikatar Harkokin kasashen Waje na daya a sai kuma Sanata Musiliu Obanikoro Minista a Ma’aikatar Labarai na Biyu.
Sauran su ne Kanar Augustine Akobundu (mai ritaya) a matsayin Minista a Ma’aikatar Tsaro, sai Mista Fidelis Nwankwo, Minista a Ma’aikatar Lafiya, yayin da Hauwa Bappa ta zama Minista a Ma’aikatar Harkokin Neja-Delta, sai Mista Kenneth Kobani, Minista a Ma’aikatar Ciniki, sai Sanata Joel Ikeya da aka nada Ministan kwadago.
Shugaba Jonathan ya sanar da tabbatar da Dokta Khaliru Alhassan a matsayin Ministan Lafiya bayan shafe watanni a matsayin mai kula da ma’aikatar bayan murabus din tsohon Ministan Farfesa Onyebuchi Chukwu.