Jonathan ya sanya wa matasa sabon kofi
A shekaranjiya Laraba ne Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya yi bikin kaddamar da sabon kofin kwallon kafa da ofishinsa ya kirkiro don matasa su rika fafatawa akansa a gasar da za a fara nan gaba kadan. Kamar yadda Ministan wasanni Tamuno danagogo ya sanar, ya ce shugaban ya sanya kofin ne don matasa ’yan […]
A shekaranjiya Laraba ne Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya yi bikin kaddamar da sabon kofin kwallon kafa da ofishinsa ya kirkiro don matasa su rika fafatawa akansa a gasar da za a fara nan gaba kadan.
Kamar yadda Ministan wasanni Tamuno danagogo ya sanar, ya ce shugaban ya sanya kofin ne don matasa ’yan kasa da shekara 18 su rika fafatawa don lashe kofin. Kuma dukkan Jihohin kasar nan 36 ciki har da Abuja ne za su shiga gasar.
Ministan ya ce makasudin sanya kofin shi ne don a rika zakulo matasa masu hazaka a fannin kwallon kafa daga sassa daban-daban na kasar nan don su rika fafatawa a kai. Ya ce yin haka ko shakka babu zai sa a rika zakulo hazikan matasa da za su rika shiga manyan kungiyoyin kwallon kafa na kasar nan don a dama da su.
A nasa jawabin, shugaba Jonathan ya bayyana farin cikinsa game da sanya sabon kofin da ofishin shugaban kasa ya dauki nauyi.
Ya ce idan aka lura da yadda kwallon kafa ke kawo hadin kai a kasar nan, inda babu bambancin addini ko kabila to abu ne da ya dace gwamnati ta fi mayar da fifiko a kai.
Shi dai kofin za a rika yin gasa a kansa ne a duk shekara, sai dai Ministan wasannin bai ambaci takaimaman ranar da za a fara yin gasar ba.
Daga cikin tsofaffin ’yan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da suka halarci bikin kaddamar da sabon kofi akwai Kanu Nwankwo da Peter Rufa’i da Taribo West da Emmanuel Babayaro da Garba Lawal da Augustine Egaboen da sauransu.