Jonathan ya yi bikin ranar haihuwar Patience bayan rasuwarta

Da a ce tana raye a bana marigayiyar ke cika shekara 57 da haihuwa.

Jonathan ya yi bikin ranar haihuwar Patience bayan rasuwarta

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar mai dakinsa, marigyayi Dame Petience duk da ba ta a raye.

A ranar 25 ga Oktoba aka ga tsohon Shugaban Kasar tare da sauran ahalinsa a wajen kwarya-kwaryar bikin da suka shirya don bikin ranar.

An ce tsohon Shugaban Kasar ya yada wani tsohon bidiyo da suka yi yayin bikin a halin rayuwar Peteince a baya don nuna murnar zagayowar wannan rana ta 25 ga Oktoba.

ROTV ta rawaito cewa, da a ce tana raye a bana marigayiyar ke cika shekara 57 da haihuwa.

A watan Satumba, 2012 aka garzaya da Patience asibitin Jamus bayan da aka yi zargin sa mata guba a abinci.

Bayan dawowarta daga asibiti aka ji ta ta ce, ta mutu ta tashi bayan kwana bakwai, wanda daga baya aka daina jin duriyarta a baina jama’a.

A karshe, marigayiyar ta yi mutuwar da ba dawowa.