Jonathan ya yi bikin sake tsayawa takara yayin da ake juyayin mutuwar dalibai

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya yi bikin sake tsayawa takara don ci gaba da shugabancin kasar nan a karkashin Jam’iyyar PDP a yayin da ake juyayin mutuwar dalibai 48 da aka kashe a harin bam a wata makarantar sakandare da ke Potiskum a Jihar Yobe. Sai dai kuma yana tsakiyar gabatar da jawabi sai […]

Jonathan ya yi bikin sake tsayawa takara yayin da ake juyayin mutuwar dalibai

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya yi bikin sake tsayawa takara don ci gaba da shugabancin kasar nan a karkashin Jam’iyyar PDP a yayin da ake juyayin mutuwar dalibai 48 da aka kashe a harin bam a wata makarantar sakandare da ke Potiskum a Jihar Yobe.

Sai dai kuma yana tsakiyar gabatar da jawabi sai ya bukaci a yi tsit na minti guda, domin nuna alhinin kisan daliban, inda ya yi alkawarin gwamnatinsa za ta dauki matakan kawo karshen tashin hankalin da ake fama da shi a Arewa.
Shugaba Jonathan ya zayyana wasu daga cikin manyan abubuwan da ya ce ya samu nasarar gudanarwa da suka hada da magance cutar Ebola. Ya ce a fannin ilimi a karkashin mulkinsa kowace shiyya a kasar nan ta samu jami’ar Gwamnatin Tarayya, haka a fannin noma manoma miliyan 14, wadanda miliyan biyu daga cikinsu mata ne sun samu takin zamani ta hanyar sakon wayar salula.
Shugaba Jonathan ya ce ya kuma kawo karshen dogayen layuka a gidajen man fetur da kuma kammala yashe kogin Neja. Sai ya ba da tabbatacin samar da wutar lantarki mai dorewa da kammala titin jirgin kasa tsakanin Kaduna da Abuja ta yadda ma’aikata za su samu saukin sufuri.
Shugaban ya ce Najeriya ta yi nasarar cimma muradin karni na Majalisar dinkin Duniya na rage yunwa da talauci shekara biyu kafin zaben 2015.
Fitattun ’yan Najeriya daga sassan siyasar kasar nan shida da suka hada da Wakilin Adamawa Alhaji Hassan Adamu da Farfesa Jerry Gana da Alhaji Attahiru Bafarawa da Cif Peter Odili da Cif Olabode George sun bayyana dalilan da ya sa ya zama wajibi a sake zaben Shugaba Goodluck Jonathan a zaben badi.

Duk abin da muke so Jonathan ya yi mana har ya kara a yankin Arewa maso Gabas –Wakilin Adamawa
Alhaji Hassan Adamu Wakilin Adamawa ya ce yankinsa na Arewa maso Gabas ba ya da abin da zai ce wa Shugabn Jonathan illa su yi ta gode masa da irin ci gaban da aka samu a yankin a lokacin mulkinsa, inda ya ce, Shugaban ya yi wa yankin duk abin da suke so har ma da kari. Alhaji Hassan Adamu ya ce lallai yanzu dole mutanen yankin su biya Shugaban a kan abubuwan da ya yi musu wajen ba shi kuri’a dari bisa dari a zaben 2015.
Jihohin Arewa maso Gabas dai su ne suka fi fama da matsalar rashin tsaro da suka hada da Adamawa da Borno da Yobe da Bauchi da Taraba da Gombe.

Za mu ba Jonathan kuri’u na fitar hankali a Arewa maso Yamma a zaben 2015 – Bafarawa
Shi kuwa tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru dalhatu Bafarawa ya tabbatar wa Shugaba Jonathan ne cewa yankin Arewa maso Yamma zai ba shi kuri’u har da na fitar hankali a zaben 2015. Alhaji Attarhiru Bafarawa ya kara da cewa mene ne kuma yankin ke bukata a wajen Shugaba Jonathan bayan irin mukaman da ya ba ’ya’yan yankin da suka hada da Mataimakin Shugaban kasa da ministoci da Sufeto Janar na ’Yan sanda da Mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, saboda haka za su ba shi duk goyon bayan da yake bukata.
Yankin Arewa maso Yamma dai ya kunshi jihohin Kaduna da Kano da Sakkwato da Zamfara da Kebbi da kuma Jigawa.
Shi kuwa Farfesa Jerry Gana ya ce Shugaba Jonathan ya farfado da sufurin jiragen kasa da inganta sufurin jiragen sama da inganta hanyoyin mota da samar da ilimi da kuma ci gaban kasa. Dokta Peter Odili kuwa godiya ya yi ga al’ummar Najeriya kan goya wa dansu baya a shekarar 2011 da kuma sake bukatar su sake goya masa baya don ci gaba da ayyukansa.
Sanata Ken Nnamani ya ce yanzu ba lokacin gwaji ba ne, saboda haka wanda ya san zurfin ruwa ya dace a ba shi damar ci gaba da ayyuka. Shi kuma Cif Olabode George ya yaba ne da karimcin Shugaban inda ya shaida masa cewar shugabansu Obafemi Awolowo da ma ya ce wata rana za a yi Shugaban kasa dan kabilar Ijaw wanda zai bada gudunmawa kuma yau hasashensa ya tabbata. Ya ce za su yi taronsu na kabilar Yarbawa inda za su bayyana goyon bayansu ga Shugaban.