Jonathan ya yi wa gwamnoni bi-ta-da-kulli
Babu wanda ya yi mamakin korar da Shugaba Goodluck Jonathan ya yi wa wasu ministoci tara a kwanakin baya domin kuwa an san za a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. Abin da kawai ya bayar da haushi game da gangancin da ya kai Jonathan yin haka shi ne, yadda ya yi ramuwar gayya, kuma […]
Babu wanda ya yi mamakin korar da Shugaba Goodluck Jonathan ya yi wa wasu ministoci tara a kwanakin baya domin kuwa an san za a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. Abin da kawai ya bayar da haushi game da gangancin da ya kai Jonathan yin haka shi ne, yadda ya yi ramuwar gayya, kuma cikin fushi. Jama’a sun dade suna jiran ya sake lale a majalisar ministoci, amma ko da ya tashi yin haka sai ga shi nan ya yi idanunsa a rufe, ya kori wadanda bai kamata ba ya kora, ya kuma kyale wadanda kowa ya zaci zai tumbuke. Kodayake Shugaba Jonathan yana da ‘yancin baiwa wanda yake so mukamin minista, ya kuma sauke wanda duk ya ga dama, amma an tabbatar da cewa ya biye wa son zuciya da ra’ayinsa na siyasa wajen sauke wadansu a ‘yan kwanakinnan.
Matsalar da ta dabaibaye jam’iyyar PDP, har tana neman ta kifar da ita kasa warwas ce ta kai Shugaba Jonathan daukar wannan matakin da zai ba shi damar wancakalar da wadanda yake tsammani suna tare da fandararrun gwamnonin da suka kafa sabuwar jam’iyar PDP. To idan har wadancan ministoci tara da aka kwabe daga mukamansu ba su iya aikinsu ba kamar yadda aka yi kazafi, to me ya sa aka kyale wasu ministocin da kowa ya san ba su tabuka wani abin kirki kaman su Diezani Allison Madueke, Nyesome Wike da kuma ‘yan koren Turawan da ke tatse arzikin kasar, kaman su Okonjo-Iweala da dai sauransu?
Abin takaici ne ganin yadda Shugaba Jonathan, wanda shi ma kansa bai tsinana komai ba a tsawon shekaru biyu bayan aringizon zaben da ya cicciba shi ya hau mulki, bai dauki matakan ingiza keyar wasu ministocin da ba su da sauran mamora a gwamnatinsa, ba su kuma da wani amfani ga al’umomin kasar nan; hasali ma daga matsayin wasu ya yi don tsananin son zuciya da tsagwaron kabilanci. A takaice dai ko yaron da aka haifa watan jiya ya san cewa Shugaba Jonathan na son muzguna wa gwamnonin da suka sanya kafar wando guda ne da shi, don ya nuna masu cewa ruwa ba sa’an kwando ne ba.
Ba wanda zai musanta cewa Shugaba Jonathan ya fatattaki tsohuwar karamar Minista a Ma’aikatar Tsaro, Mrs Olusola Obada ne domin kasancewarta mataimakiyar Gwamna Olagunsoye Oyinlola, tsohon Sakataren jam’iyyar PDP, wanda a yanzu haka shi ne babban sakataren sabuwar PDP, kuma na hannun daman Olusegun Obasanjo, kamar yadda tsohon ministar harkokin kasashen waje, Gbenga Ashiru ya kasance. Ashe ke nan ana iya cewa Shugaba Jonathan ya yi wa tsohon ubangidansa ne bi-ta-da-kulli.
Abin da wannan rashin karimcin da Shugaba Jonathan ya yi wa gwamnonin sabuwar jam’iyar PDP da makararrabansu ya nuna cewa ya kama hanyar yakin neman zabe ne a gigice, kamar zakin da aka harba wajen farauta, wanda duk ya shiga gabansa zai gamu da gamonsa. Dangane da haka yanzu kowa ya zura ido ya ga yadda za a canja wadancan ministoci da sababbin da za a zakulo daga bangaren tsohuwar PDP, domin su ne za su zame ‘yan daukar garar amarya, inda aka ce su sauke, su sauke.
Sai dai akwai ranar kin cin dillanci, wato ranar da hajar Maigari ta bace. Yanzu ba a maganar ra’ayin jama’a, abin da ran Shugaba Jonathan ya raya shi ne ke zama umurnin da jami’an gwamnati da kuma shugabannin PDP za su bi tilas. Duk da cewa wadancan ministocin da aka ga bayansu, gwamnonin jihohinsu ne, ko kuma a ce iyayen gidansu da ke da ruwa da tsaki ne a harkokin gudanar da jam’iyya, suka amince aka nada su, sai ga shi za a koma ta kan karan-kada-miya ne a wadancan jihohin don su bayar da sunayen wasu jigari-jigarin da aka tabbatar gwanaye ne wajen amshin Shata, a nada ministocin je-ka-na-yi-ka, wadanda ba za su furta komai da yawun jama’ar jihohinsu ba, sai dai abin da za a tursasa su aikatawa.
A yanzu dai kamata ya yi a ce cikakken garambawul ne Shugaba Jonathan ya yi don a kawar da rubabbun kayar da ke dankare a majalisar ministocinsa, a maye gurabansu da wadanda kwakwalwarsu ke harbawa, jininsu na bugawa yadda ya kamata, suna kuma yin kazar-kazar cikin hanzari don ceto kasar nan daga illoli da rashin tabukawar gwamnati suka haifar. A yanzu dai talakawa sun cire rai ga samun sa’ida daga wadanda ke jan ragamar kasar nan, sun dukufa fatan samun wasu da za su maye gurbinsu don ficewa daga bakar fitina da kangin ukubar gwamnatin Jonathan.