Jonathan ya yi wa kungiyar Boko Haram tayin sulhu

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya mika wa kungiyar Boko Haram tayin sulhu a jawabin da ya gabatar wa jama’ar kasa a shekaranjiya Laraba don murnar bikin cika shekara 54 da samun mulkin kan Najeriya.Shugaban ya ce, gwamnatinsa a shirye take ta saurari wadanda suke da korafi na gaskiya domin dawo da zaman lafiya a […]

Jonathan ya yi wa kungiyar Boko Haram tayin sulhu
Jonathan ya yi wa kungiyar Boko Haram tayin sulhu

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya mika wa kungiyar Boko Haram tayin sulhu a jawabin da ya gabatar wa jama’ar kasa a shekaranjiya Laraba don murnar bikin cika shekara 54 da samun mulkin kan Najeriya.
Shugaban ya ce, gwamnatinsa a shirye take ta saurari wadanda suke da korafi na gaskiya domin dawo da zaman lafiya a kasar nan.
Ya ce, “Wannan gwamnati ta sadaukar da kanta wajen tabbatar da daukacin ’yan Najeriya suna zaune lafiya a ko’ina ba tare da lura da wurin haihuwa ko addinin da suke bi ko jam’iyyun da suka fito. Ga wadanda suka kaddamar da yaki kan kasarmu, ina kiranku kan ku ajiye makamanku, ku rungumi zaman lafiya.”
Shugaba Jonathan ya kara da cewa, “Wadanda suke da korafi na gaskiya, ina tabbatar musu Najeriya zai ta saurare su, idan kuka gabatar da korafinku a kan teburi domin tattaunawa a kai.”
Ya kara da cewa, “Ga mutanen Najeriya, ina sake nanata cewa aikin da ke kanmu na gina ingantacciyar Najeriya don zama gagaruma ba zai tafi a banza ba.”
Shugaban ya nuna damuwa kan cewa duk da rawar da gwamnatinsa take takawa har yanzu Najeriya tana fama da matsaloli. Ya jingina halin da kasar take ciki kan ayyukan ’yan Boko Haram, wadanda ya ce suna kawo babban kalubale ga hadin kan kasar nan.
“A jawabina na bara, na nanata cewa muna cikin damuwa a kasar nan. Kuma har yanzu muna cikin wannan hali duk da irin kokarin da gwamnatinmu ke yi. Damuwarmu ya shafi rikice-rikicen da kasarmu ke ciki, sakamakon ayyukan ’yan ta’adda wadanda suke kawo mummunan barazana ga hadin kanmu a matsayin al’umma,” inji Shugaban kasar.
Sai dai ya ce yakin da ’ya’yan kungiyar suka kaddamar kan kasar, ba za su samu nasara ba, inda ya ce abubuwan da suke yi ya kawar da shakkun mai shakku cewa ’yan ta’adda ba su nufin alheri ga kowa ko wani addini ko gwamnati
Ya bayyana zabinsu na raunanawa da jefa jama’a a cikin wahala ta hanyar kai miyagun hare-hare da cewa alama ce ta rashin imani.
Shugaban ya bukaci daukacin ’yan Najeriya su ajiye bambancin siyasa da na yanki da sauran bambance-bambance su goyi bayan kokarin gwamnati da na sojoji wajen magance hare-haren.
Ya yi alkawarin aiwatar da shawarwarin Taron kasa na Shekarar 2014 wanda ya bayyana da tukuicin shekara dari ne da ya kamata a yaba tare da aiki da shi.
Da ya juya kan zaben 2015 da ke gabatowa Shugaba Jonathan ya bukaci ’yan siyasa su sani cewa takarar neman shugabanci ba yana nufin ruguza siyasar ba ce. “Kamata ya yi takarar neman mukaman mulki su haifar dda kyakkyawan shugabanci ba bada damar kasa ta koma kamar ba shugabanci ba. Son kasa ya zamo a sama da bukatun daidakunmu,” inji shi.
Ya yi alkawarin sadaukar da kai wajen dorewar Najeriya a matsayin kasa daya mai bin akidar dimokuradiyya na kare hakkin daidaikun jama’a da bayar da ’yanci da tabbatar da adalci a gaban doka da zabin bayyana ra’ayi.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi