…Jonathan zai ciyo bashin Naira biliyan 168 don yaki da Boko Haram
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya aike wa Majalisar Dokoki ta kasa bukatar ta sahale masa ya ciyo bashin Dala biliyan daya (kimanin Naira biliyan 168) don yaki da kungiyar Boko Haram.Wata takarda da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Dabid Mark, Shugaba Jonathan ya yi magana kan bukatar nemo bashi daga kasashen waje […]
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya aike wa Majalisar Dokoki ta kasa bukatar ta sahale masa ya ciyo bashin Dala biliyan daya (kimanin Naira biliyan 168) don yaki da kungiyar Boko Haram.
Wata takarda da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Dabid Mark, Shugaba Jonathan ya yi magana kan bukatar nemo bashi daga kasashen waje don inganta samar da kayan yaki domin a yaki hare-haren da suke aukuwa a sassan Najeriya musamman a Arewa maso Gabas.
Shugaba Jonathan ya kuma ce za a yi amfani da wani bangare na kudin wajen horar da sojoji da sauran jami’an tsaro.
“Na san ba ku da shakku kan kalubalen tsaro da kasar nan ke fama da shi, musamman barazanar da hare-haren Boko Haram ke haifarwa. Wannan lamari ne da muka sha tattaunawa a lokuta da dama. Kuma ina son jawo hankalinku kan bukatar da ke akwai ta gaggauta inganta samar da makamai da horar da sojoji da sauran jami’an tsaro domin ba su damar fuskantar wannan babbar barazana da karfinsu.”
Ya ci gaba da cewa, “Bisa wannan dalili nake bukatar amincewar Majalisar Dokoki ta kasa don ciyo bashin Dala biliyan daya da zai hada da tsari a tsakanin gwamnati da gwamnati don ingantawar.”
Ya ce yana fata ’yan majalisar za su gagauta ba shi goyon wajen karbo bashin kudin.
Ciyo bashin daga waje ya zo ne a daidai lokacin da ake suka tare da neman bayani kan yadda ake tafiyar da kasafin tsaron Najeriya wanda ya lashe kusan rubu’in daukacin
kasafin kasar nan a shekara biyu da suka gabata.
Gwamnati tana kashe kimanin Naira tiriliyan daya kan tsaro a daidai lokacin da harkokin tsaro ke dada tabarbarewa a kasar nan. Yayin da sojoji da sauran jami’an tsaro ke ci gaba da kokawa cewa rashin ingantattun kayan aiki ne ke hana su murkushe hare-haren Boko Haram.