Jonathan zai fuskanci dakatarwa daga PDP saboda nasarar APC
Ziyarar da Shugabannin APC suka kaiwa Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan, a masaukinsa da ke Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa cikin ziyarar harda shugaban APC na kasa Adam Oshiomhole, jam’iyyar PDP da ta sha kaye a zaben Gwamnan jihar da aka yi ranar Asabar ta zargi Jonathan da hada kai wajen faduwar PDP a […]
Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan
Ziyarar da Shugabannin APC suka kaiwa Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan, a masaukinsa da ke Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa cikin ziyarar harda shugaban APC na kasa Adam Oshiomhole, jam’iyyar PDP da ta sha kaye a zaben Gwamnan jihar da aka yi ranar Asabar ta zargi Jonathan da hada kai wajen faduwar PDP a jihar.
Don haka jam’iyyar PDP ta ce, akwai yiwuwar a dakatar da tsohon shugaban daga jam’iyyar PDP saboda nasarar da Dan takarar APC David Lyon, ya samu a zaben Gwamnan jihar.