Jonathan zai iya korar kowa a kan Diezani – Sarki Sanusi

Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya ce tsohon Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan zai iya korar kowa daga kan mukaminsa idan ya aibata tsohuwar Ministar Man fetur Diezani Allison-Madueke.Gidan rediyon BBC ya ce Sarki Sanusi II, wanda ya bayyana haka a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Forbes Africa, […]

Jonathan zai iya korar kowa a kan Diezani – Sarki Sanusi
Jonathan zai iya korar kowa a kan Diezani – Sarki Sanusi

Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya ce tsohon Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan zai iya korar kowa daga kan mukaminsa idan ya aibata tsohuwar Ministar Man fetur Diezani Allison-Madueke.
Gidan rediyon BBC ya ce Sarki Sanusi II, wanda ya bayyana haka a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Forbes Africa, ya kara da cewa sanin haka ne ya sa ya shirya sauka daga mukaminsa na Gwamnan Babban Bankin Najeriya, a lokacin da ya kai karar ta wajen tsohon Shugaban kasar.
Tsohon Gwamnan Babban Bankin dai ya aike wa Jonathan wasika, inda ya shaida masa cewa Kamfanin Man fetur bai sanya Dala biliyan 49 na kudin man da ya sayar a asusun gwamnati ba, amma tsohon Shugaban kasar bai ce masa komai a kai ba.
A cewar Sarki Sanusi II, Jonathan ya yi magana a kan batun ne kawai sakamakon wasikar da tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya rubuta wasa, wacce aka wallafa a jaridu da dama na kasar nan, inda ya bukaci ya dauki mataki a kan zarge-zargen satar da ake yi a kamfanin man fetur din.