Jonathan zai mika wa Buhari mulki 28 ga Mayu

Shugaban kasa mai barin gado Dokta Goodluck Jonathan zai mika ragamar shugabancin kasar nan gaa Janar Muhammadu Buhari a ranar 28 ga watan Mayu maimakon 29 ga watan. Shugaban kasar ya yanke wannan shawara ce a zaman Majalisar Zartarwa ta kasa a shekaranjiya Laraba a Abuja, Ministar Watsa labarai Misis Patricia Akwashiki ta shaida wa […]

Jonathan zai mika wa Buhari mulki 28 ga Mayu
Jonathan zai mika wa Buhari mulki 28 ga Mayu

Shugaban kasa mai barin gado Dokta Goodluck Jonathan zai mika ragamar shugabancin kasar nan gaa Janar Muhammadu Buhari a ranar 28 ga watan Mayu maimakon 29 ga watan.

Shugaban kasar ya yanke wannan shawara ce a zaman Majalisar Zartarwa ta kasa a shekaranjiya Laraba a Abuja,
Ministar Watsa labarai Misis Patricia Akwashiki ta shaida wa manema labarai na fadar Shugaban kasa cewa gwamnatin Jonathan ta shirya liyafa a ranar 28 ga watan Mayu domin mika wa Janar Buhari mulkin Najeriya.
Sai masana shari’a sun yi sabani kan lokacin da mulkin Jonathan zai kare da kuma lokacin da Buhari zai amshi ragamar mulkin.
Yayin da Farfesa Awwalu Yadudu ke da ra’ayin cewa wa’adin mulkin Jonathan zai kare ne a daren 28 ga Mayu, Samuel Okutepa yana da ra’ayin wa’adin mulkin zai kare ne daren 29 ga Mayu, sai dai idan ya yanke shawarar yin murabus.
Ya ce, a aikace a lokacin mika mulki Abdulsalami Abubakar ya mika wa Obasanjo mulki a ranar 29 ga Mayun 1999, don haka aiwatar da rantsuwar kama mulki na Buhari za ta fara aiki ne a ranar 29 ga Mayu.
“Na tuna mika mulkin Janar Abdulsalami Abubakar ga Obasanjo. Wa’adin zai kare ne a tsakiyar daren 28 ga Mayu,” inji Yadudu.
Ya ce, abin da tsarin mulki yake bukata mulkin ba zai fara aiki ba, sai an yi rantsuwar kama aiki.
Shi kuwa Otukepa ya ce, wa’adin Buhari zai fara ne dakika daya da shiga ranar 30 ga Mayu, inda ya ce, babu laifi idan Jonathan ya yanke shawarar mika mulki da safe ko da rana a ranar 29 ga Mayu, inda ya ce, wa’adinsa zai kare ne da misalin karfe 11:59 na daren ranar.
Ya ce, a bisa ilimin shari’a Buhari zai zama Shugaban kasa ne a ranar 30 ga Mayu, don haka Jonathan zai iya sauka daga mulki ne kawai a ranar 28 ga Mayu idan ya yanke shawarar yin murabus.
Sai dai Ministar ta ce Shugaban kasar zai mika harkokin kasar nan ga Buhari ne a wajen wata liyafar cin abincin dare ana gobe 29 ga Mayu Ranar Dimokuradiyya.
“A ranar 28 ga Mayu, Shugaban kasa ya shirya liyafar mika mulki ta yadda zai bar 29 ga Mayu ga gwamnati mai zuwa. A ranar 28 ga Mayu muna fatar samar da hanyar shugabanci guda tare da yin maraba da sabuwar gwamnati. Kuma kun san ranar 29 ga Mayu, ranar dimokuradiyyarmu ce. Don haka mun tsara ayyukan da za a gudanar a daukacin wannan mako, kamar nuna nasarorin da muka samu da sauran abubuwan da muke yi a Ranar Dimokuradiyya, sai dai wannan shekarar ta musamman ce mai dauke da kaddamar da sabon Shugaban kasarmu da ke zuwa a ranar 29 ga Mayu,” inji ta.
Wakilinmu ya ruwaito cewa Ministar albarkatun man fetur, Dizeani Alison-Madueke da takwararta ta kudi, Ngozi Okonjo-Iweala, bas u halarci zaman majalisar ba, wanda shi ne na farko bayan Jonathan ya sha kasa a hannun Janar Buhari a zaben da aka gudanar ranar 28 ga Maris.