Jonathan zai nada Shekarau minista

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya mika wa Majalisar Dattawa sunan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau domin nada shi a matsayin minista.Shugaban ya kuma mika sunayen Dokta Abdul Bulama daga Jihar Yobe da Yarima Dayo Adeyeye daga Jihar Ekiti da kuma Steben Oruh daga Jihar Delta don neman amincewar majalisar ya ba su […]

Jonathan zai nada Shekarau minista
Jonathan zai nada Shekarau minista

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya mika wa Majalisar Dattawa sunan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau domin nada shi a matsayin minista.
Shugaban ya kuma mika sunayen Dokta Abdul Bulama daga Jihar Yobe da Yarima Dayo Adeyeye daga Jihar Ekiti da kuma Steben Oruh daga Jihar Delta don neman amincewar majalisar ya ba su mukaman ministoci. A bana ne tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya sauya sheka daga Jam’iyyar APC zuwa Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar nan. Kuma a mako mai zuwa ne ake sa ran Majalisar Dattawan za ta fara tantance sunayen mutanen da aka mika mata domin zama ministocin.