Jontahan ya yi alkawari hada Katsina da titin jirgin kasa
Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce gwamnatinsa za ta yi titin jirgin kasa daga Kano zuwa Katsina. Shugaban ya furta haka ne a fadar Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman a ziyarar yini biyu da ya kai Jihar Katsina a makon jiya. Shugaba Jonathan ya ce gwamnati na shirin kai layin dogo a […]

Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce gwamnatinsa za ta yi titin jirgin kasa daga Kano zuwa Katsina. Shugaban ya furta haka ne a fadar Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman a ziyarar yini biyu da ya kai Jihar Katsina a makon jiya.
Shugaba Jonathan ya ce gwamnati na shirin kai layin dogo a dukkan manyan biranen jihohin kasar nan.
Shugaban ya ce ba don irin gudunmawar da Katsinawa suka ba shi ba da yanzu yana can jiharsa ta Bayelsa a matsayin Gwamna don haka ne yake alfahari da jihar. Sai ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta yi bakin kokarin samar wa jama’ar jihar da ruwan sha a birane da karkara tare da inganta harkokin noma.
Tun farko a jawabinsa, Sarkin Katsina ya nemi a hada birnin Katsina da layin jirgin kasa daga Jihar Kano. Sarkin ya ce akwai wannan yunkuri tun 1979.
Sarkin ya kuma yi kira ga Shugaban kasa ya kokarta wadatar da al’ummar jihar da ruwa tare da gyara manyan madatsun ruwa na Zobe da Jibiya da Ajiwa don habaka harkokin noma.
Alhaji Abdulmumini Usman ya kuma yi kira ga Shugaban kasa dangane da dawo da zaman lafiya tare da tsaida kashe-kashen da ake yi a Arewa.
A yayin ziyarar, Shugaba Jonathan ya bude hanyar da ta yi wa babban birnin zobe tare da asibitin kashi da katafaren sabon gidan gwamnati da ya ci Naira biliyan 8 da filin wasa na zamani da wajen koyar da sana’o’i da sauran ayyukan da gwamnatin Barista Ibrahim Shema ta gudanar.
Shugaban ya kuma ziyarci Hajiya Dada, mahaifiyar marigayi Shugaba Umaru Musa ’Yar’aduwa a gidansu da ke Unguwar ’Yar’aduwa a cikin garin Katsina, inda ya shaida mata cewa shi ma uwa ce ita a gare shi, saboda ba don danta ba da bai hau wannan kujera ta shugabancin kasar nan ba.