Jordan ta rufe iyakarta da Iraki da Siriya

kasar Jordan ta ayyana rufe kan iyakarta da kasashen Siriya da Iraki, sakamakon mummunan harin bam din da ya hallaka sojojinta shida ranar Talata.An kaddamar da harin ne daga bangaren kasar Siriya kusa da sansanin ‘yan gudun hijira.Gwamnatin kasar Jordan ta ce ba za a sake gina sabbin sansanonin ‘yan gudun hijrar ba, kana ba […]

Jordan ta rufe iyakarta da Iraki da Siriya
Jordan ta rufe iyakarta da Iraki da Siriya

kasar Jordan ta ayyana rufe kan iyakarta da kasashen Siriya da Iraki, sakamakon mummunan harin bam din da ya hallaka sojojinta shida ranar Talata.
An kaddamar da harin ne daga bangaren kasar Siriya kusa da sansanin ‘yan gudun hijira.
Gwamnatin kasar Jordan ta ce ba za a sake gina sabbin sansanonin ‘yan gudun hijrar ba, kana ba za a fadada ko guda ba,kamar yadda BBC ta bayyana.
Gomman mutane ne ke gudanar da taron addu’oin tare da kunna kyandira a Amman, babban birnin kasar, don tunawa da wadanda harin ya rutsa da su.
Babu dai tabbaci kan ko su wanene ke da alhakin kaddamar da harin.
Har ila yau, a farkon watan nan ne gwamnatin kasar ta ce mutane biyar ne suka mutu sakamakon harin da aka kai ofishin leken asiri da ke sansanin ‘yan gudun hijirar Palasdinawa mafi girma a kasar.
Wani mai magana da yawun gwamnatin ya ce cikin wadanda suka mutu har da jami’an leken asiri uku a sansanin na Bakaa da ke kusa da birnin Amman.