Jos ta Arewa: Kotun Daukaka kara ta soke zaben Hon. Agah
Kotun daukaka karar ta tabbatar da Muhammad Adam Alkali na Jam’iyyar PRP a matsayin zababben dan Majalisar Tarayyar mai wakiltar mazabar.
Majalisar Wakilai
- NAJERIYA A YAU: Yadda Sauya Takardun Naira Za Ta Shafe Ku
- Kotu ta yanke wa wanda ya kashe abokinsa hukuncin rataya
Kotun daukaka karar sanar da haka ne bayan ta yi watsi da karar da Honorabul Musa Avia Agah ya daukaka zuwa gabanta yana kalubalantar hukuncin kotun kararrakin zabe da ta soke zabensa a tun ranar 2 ga watan Satumba.
Kotun ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana Muhammad Adam Alkali na PRP a matsayin wanda ya lashe zaben sannan ta mika masa takardar shaidar cin zaben mazabar.
Hon Agah ya daukaka kara zuwa kotun ne yana neman so ta yanke hukunci ko kotun baya ta yi daidai wajen cewa ba a yi zaben sa a matsayin dan takara ta halasciyar ba, sannan ko ya dace a ayyana Alkali a matsayin wanda ya ci zabe.
Ta bayyana cewa jam’iyyar PDP ta saba umarnin Babbar Kotun Jihar Filato na gudanar da babban taronta, don haka ba ta cika sharadin tsayar da dan takara ba.