Jose Mourinho ya sake zama kocin kulob din Chelsea
A ranar Litinin da ta gabata ne kulob din Chelsea da ke Ingila ya fitar da sanarwar daukar Jose Mourinho a matsayin kocinsa wanda zai maye gurbin Rafa Benitez.Kulob din ya ce tuni ya kulla yarjejeniya da Mourinho inda zai shafe shekara hudu a kulob din a matsayin koci.Mourinho, mai kimanin shekara 50, ya taba […]
A ranar Litinin da ta gabata ne kulob din Chelsea da ke Ingila ya fitar da sanarwar daukar Jose Mourinho a matsayin kocinsa wanda zai maye gurbin Rafa Benitez.
Kulob din ya ce tuni ya kulla yarjejeniya da Mourinho inda zai shafe shekara hudu a kulob din a matsayin koci.
Mourinho, mai kimanin shekara 50, ya taba zama kocin kulob din a tsakanin shekarar 2004 zuwa 2007 don haka za a iya cewa shi ba bako ba ne a kulob din.
dan asalin Fotgual, Mourinho ya lashe kofin gasar rukunin Premier na Ingila sau biyu a jere a wancan lokaci bayan da kulob din ya shafe shekaru masu yawa ba tare da lashe kofin ba.
Babban jami’i a kulob din mai suna Ron Goulay ya bayyana Mourinho a matsayin wanda magoya bayan kulob din ke kauna musamman wajen sunan da ya yi da kuma irin nasarorin da ya samu a harkar horarwa.
Ana sa ran a ranar Litinin 10 ga watan Yuni mai zuwa ne kulob din zai tabbatar da shi a matsayin koci a taron ’yan jaridu da za a yi a filin wasa na Stamford Bridge kuma daga nan ne zai fara aiki gadan-gadan.
Tuni Mourinho ya isa kulob din da uku daga cikin masu taimaka masa a harkar horarwa da suka hada da Rui Faria da Silbino Louro da kuma Jose Morais.